Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeAddiniKotu ta umarci...

Kotu ta umarci Sheikh Abduljabbar ya gabatar da litattafan da ya yi amfani da su wajen kafa hujja a shari’ar farko

Babbar kotun jihar Kano mai sauraron ƙorafe-ƙorafen ɗaukaka ƙara ta saurari ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar yana ƙalubalantar hukuncin kisa da Kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu ta yanke masa kan zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A zaman kotun da aka gudanar, lauyoyin ɓangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu, inda lauyoyin Sheikh Abduljabbar suka roƙi kotun da ta soke hukuncin da aka yanke masa tare da wanke shi daga zargin.

Ku kuma karanta: Farfesa Mansur Yelwa ya sauka daga limancin masallacin jami’ar ATBU

Sai dai lauyoyin gwamnatin jihar sun buƙaci kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Nasir Saminu, ya umarci a gabatar masa da wasu litattafai da aka yi amfani da su a shari’ar kotun farko domin ci gaba da nazarin ƙarar.

Rahotanni sun ce kotun za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar a wani lokaci mai zuwa.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

‘Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro

'Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro ‘Yan sanda da sojoji sun tare tsoffin jami’an tsaro da suka yi ƙoƙarin gudanar da zanga-zanga a Ma’aikatar Tsaro kan batun rashin biyan wasu kuɗaɗen gyaran fansho da suke...

Alaƙa tsakanin Isra’ila da Qatar na ƙara tsami: Isra’ila ta haramta fitar da kayayyakin masana’antun sojinta zuwa Qatar

Alaƙa tsakanin Isra’ila da Qatar na ƙara tsami: Isra'ila ta haramta fitar da kayayyakin masana’antun sojinta zuwa Qatar Rahotanni daga Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin hana fitar da duk wani samfurin da ya shafi masana’antun sojojinta zuwa...

Amurka ta bayyana mutane 5 da suka kai hare-hare ta intanet a kan muhimman cibiyoyin ta

Amurka ta bayyana mutane 5 da suka kai hare-hare ta intanet a kan muhimman cibiyoyin ta Gwamnatin Amurka ta fitar da wata sanarwa mai cike da ƙayatarwa a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta bayyana sunayen mutane biyar da...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.