Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

HomeIlimi'Yar shekaru 24,...

‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a da sakamako mafi daraja

‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a da sakamako mafi daraja

Wata matashiya mai shekaru 24, Aisha Widad Yahaya, wadda ita ce uwa ga yaro ɗaya kuma matar aure, ta kafa tarihi a Jami’ar Bayero Kano (BUK) bayan ta kammala karatun Digirin Shari’a (Law) da Ajin Farko (First Class Honours), abin da babu wani ɗalibin wannan tsangaya da ya samu cikin shekaru 35 da suka gabata.

Aisha, wadda aka haifa a ranar 3 ga Yuli, 2001, a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, ta fara karatu a Makarantar Firamare ta Al-Azhar, sannan ta kammala sakandare a Musa Ilyasu College. Daga bisani ta samu gurbin karantar Shari’a a Jami’ar Bayero Kano, matakin da ta ce ya samo asali ne daga ƙwarin gwiwar mahaifinta marigayi Farfesa Dahiru Yahaya, fitaccen masanin tarihi kuma tsohon malami a jami’ar.

A cewarta, ba ta shiga jami’a da burin karya wani tarihi ba. Sai dai bayan da ta samu cikakkiyar maki 5.0 (GPA) a shekararta ta biyu, sai ta fahimci cewa za ta iya kammala karatu da Ajin Farko a Digirinta. Daga nan ne ta ƙara himma tare da mayar da hankali wajen cimma wannan buri.

Ku kuma karanta: An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

Aisha ta bayyana cewa haɗa nauyin aure, renon ɗa da kuma karatun Shari’a mai tsauri ba abu ne mai sauƙi ba. Ta ce nasarar da ta samu ta samo asali ne sakamakon cikakken goyon bayan mijinta, iyalanta, malamanta da kuma masu ba ta shawara, waɗanda suka ci gaba da ƙarfafa mata gwiwa a tsawon tafiyarta ta ilimi.

A matsayinta na ɗa ta 18 cikin ‘ya’ya 25 na iyalinsu, kuma uwa ga yaro ɗaya, Aisha ta nuna cewa jajircewa, ɗa’a da haƙuri na iya taimakawa mutum ya shawo kan duk wata matsala.

Nasarar da ta samu ba kawai ta zama tarihi a gare ta ba, har ma ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga ɗalibai a faɗin Najeriya, tana nuna cewa babu wani buri da ba zai yiwu a cimma ba idan aka haɗa ƙwazo, sadaukarwa da jajircewa.

Taya murna ga Aisha Widad Yahaya bisa wannan gagarumar nasara, wadda ta rubuta sunanta cikin tarihin Jami’ar Bayero Kano tare da zama abin koyi ga matasa masu neman ilimi.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Babban Malami a FCE Potiskum, Dakta Mamuda ya rasu, yana da shekaru 62

Babban Malami a FCE Potiskum, Dakta Mamuda ya rasu, yana da shekaru 62 Al'ummar garin Potiskum sun shiga cikin makoki da juyayi na rasuwar Dakta Abdullahi Mamuda, Babban Malami a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCET), Potiskum. Dakta Mamuda ya rasu a...

‘Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro

'Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro ‘Yan sanda da sojoji sun tare tsoffin jami’an tsaro da suka yi ƙoƙarin gudanar da zanga-zanga a Ma’aikatar Tsaro kan batun rashin biyan wasu kuɗaɗen gyaran fansho da suke...

Alaƙa tsakanin Isra’ila da Qatar na ƙara tsami: Isra’ila ta haramta fitar da kayayyakin masana’antun sojinta zuwa Qatar

Alaƙa tsakanin Isra’ila da Qatar na ƙara tsami: Isra'ila ta haramta fitar da kayayyakin masana’antun sojinta zuwa Qatar Rahotanni daga Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin hana fitar da duk wani samfurin da ya shafi masana’antun sojojinta zuwa...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.