Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeLabariAn yi jana'izar...

An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

‘Yan’uwa Musulmi, Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da jana’izar ‘yan’uwa biyar a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ranar Laraba, 21 ga Safar, 1448AH, daidai da 5 ga Agusta, 2026. Waɗannan mutane sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Tattakin Arba’een na Imam Husaini (A.S) na shekarar 1448AH/2026 a Abuja.

Wakilin ‘yan’uwa Musulmi, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Da’irar Zariya da Kewaye, Sheikh Abdulhameed Bello, ne ya jagoranci sallar jana’izar. Bayan kammala sallar, Hurras sun gudanar da faretin girmamawa gare su.

Daga nan aka zagaya da gawarwakin zuwa Mashhadin Shuhada’u na Harkatul Islamiyya tare da faretin girmamawa, kafin daga bisani a bizne su a maƙabartar shahidan Harkar Musulunci da ke Dambo, Zariya.

‘Yan’uwan sun taso ne daga garin Udawa, wani gari da ke maƙwabtaka da Birnin Gwari a Jihar Kaduna. Hatsarin ya faru ne a daren Lahadi, 2 ga Agusta, 2026, a wani gadar ruwa da ke garin Azara, kusa da shiga Jere.

Ku kuma karanta: Miliyoyin ‘Yan’uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba’een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS)

A nan take mutum guda ya rasu, yayin da ruwa ya kwashe sauran. Bayan kwana biyu na ci gaba da gudanar da bincike a cikin ruwa, an yi nasarar gano gawarwakinsu. Har ya zuwa yanzu akwai mutum 5 da su kuma suka jikkata suna karɓar magani.

Al’amarin ya faru a daidai wata Gada ruwa, da ke gab da shiga garin Jere, bayan faɗawar motan cikin ruwa mutane 4 an samu nasarar ceto su ruwan nan take, da gangar jikin mutum ɗaya ya rasu, sauran 4 ruwa ya tafi da su. Bayan kwana biyu da aukuwar lamarin an yi nasara gano gawarwakin sauran mutun 4 inda aka yi masu Jana’iza.

Waɗanda wannan lamarin ya shafa sun hada da Hussaini M Nuhu Udawa da Abdullahi Mahmud Udawa da Aliyu Muhammad (Monitor) Uduwa da Adamu Abdullahi Uduwa da kuma Mubarak Umar Udawa.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Miliyoyin ‘Yan’uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba’een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS)

Miliyoyin 'Yan'uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba'een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS) Miliyoyin 'yan'uwa Musulmi na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun fara tattakin Yaumul Arba'een na na Imam Husaini (AS) wanda suka saba...

‘Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe ‘yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata

'Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe 'yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata Rundunar 'yan sandan ta bayyana mutumin a matsayin Kabir Sani mazaunin unguwar rukunin gidajen 'Shagari Low-Cost'. 'Yansandan sun ce maƙwabtan Kabir...

Kotu a Kano ta yanke wa Amarya hukuncin kisa kan kashe Angonta bayan kwana 9 da aure

Kotu a Kano ta yanke wa Amarya hukuncin kisa kan kashe Angonta bayan kwana 9 da aure Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Maryam Sabo, ta yanke wa Saudat Idris hukuncin kisa...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.