Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar

2
1622

Kungiyar ɗalibai ta ƙasa a Sudan, ta yi ƙira ga hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, (NIDCOM), da ta yi ƙoƙarin kwashe su daga Sudan.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Gabriel Odu, sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NIDCOM, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Mista Odu ya ce kiran na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da ɗaliban suka aikewa hukumar. Ya ce hukumar ta samu takardar neman korar mutanen musamman waɗanda ke birnin Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutumin da ya yi tattaki daga Najeriya zuwa Saudiyya a kan keke yayi karanbatta da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga

Tun da farko, Abike Dabiri-Erewa, shugabar NIDCOM, ta bayyana damuwarta kan halin da ɗaliban Najeriya ke ciki a Sudan.

Misis Dabiri-Erewa ta ce tashin hankalin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da ƙungiyar Rapid Support Forces, RSF, na da matuƙar damuwa.

Hukumar ta ba da tabbacin cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA mai kula da kai ɗaukin gaggawa na tuntuɓar tawagar Najeriya dake Sudan da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Misis Dabiri-Erewa ta buƙaci ɗaukacin ɗaliban Najeriya da ke Sudan da kuma ‘yan Najeriya mazauna Sudan, da su kasance masu lura da tsaro kuma su natsu.

2 COMMENTS

Leave a Reply