Ɗaliban Jami’ar Maryam Abacha MAAUN sun ƙirƙiri manhajar sada zumunta

0
120

Tsofaffin ɗaliban Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maraɗi a jamhuriyyar Nijar sun bayyana cewa sun ƙirƙiri wata manhaja wacce al’umma za su yi amfani da ita wajen sada zumunta a tsakaninsu.

Manhajar wacce suka sanya wa suna da ‘Afrister’, sun ce manhaja ce da aka ƙirƙira da za ta kawo sauyi wajen bai wa al’ummar damar ƙulla alaƙa da hulɗar zamantakewa.

Sun ƙara da cewa an tsara manhajar ta yadda za ta haɓaka hulda a tsakanin daidaikun mutane, iyalai, abokai, da abokan kasuwanci, wanda zai haɓaka ƙwarewar masu amfani da manhajar.

An ƙirƙiri manhajar ne a cikin shekarar 2021, a lokacin da Aliyu Ishaq da abokin aikinsa Alhassan Abubakar suke karatunsu a jami’ar MAAUN.

KU KUMA KARANTA: Menene manhajar ‘Kapo drive’?

A cewarsu Afrister ya sami karɓuwa cikin sauri a wurin masu amfani da shi ganin yadda manhajar ta zo da sabbin abubuwa masu kayatarwa.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja, Aliyu Ishaq ya danganta nasarar Afrister da irin horon da suka samu a jami’ar Maryam Abacha.

Ya nuna matuƙar godiyarsa ga jami’arsa da ya kammala, inda ya bayyana irin tasiri da jami’ar ta yi masa tare da sauran ɗalibai.

Ya kuma yabawa wanda ya assasa jami’ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo bisa irin goyon baya da jagorancin da yake bayarwa.

Domin ganin sun samu yabo da karɓuwa a duniya, Ishaq da abokin aikinsa sun ce suna aiki tuƙuru domin haɓaka Afrister, tare da tabbatar da cewa ya dace da ƙa’idodin da takwarorinsa na Yamma suka gindaya.

Ya ƙara da cewa, suna da himma da kuma ƙudurin yaɗa Afrister a duniya, wanda ya ce idan suka yi hakan, za su samu wani gagarumin ci gaba a bangaren masana’antar fasaha da manhajar ƙulla zamantakewa.

Leave a Reply