Ƙungiyar tallafawa marayu ta Jama’atul Nasirul Yatama Kudan ta baiwa marayu tallafi

0
99

Daga Idris Umar, Zaria

Ƙungiyar taimakon marayu na garin Kudan dake jihar kaduna ta shirya taron rabawa marayu kayan masarufi da suturun sallah.

Taron wanda aka yi shi a harabar makarantar firamare ta garin Kudan (MPS) kuma taron ya samu halartar manyan baƙi na ciki da wajen garin Kudan.

Cikinsu akwai Sarkin yaƙin Zazzau wanda ya wakilci mai martaba sarkin Zazzau Ambassador Nuhu Bamalli. Tukuran Zazzau Hakimin gundumar Kudan Alhaji Halliru Mahmud.

Hakimin gundumar Hunƙuyi Alhaji Aminu Ashiru, Sarkin Kudan, sarkin Nasarawar Kudan, Sarkin Ɗan Taro da sarkin Bagadi duk suna cikin mahalarta.

Kamar kowace shekara bana ma an ƙaddamar da littafi wanda Dakta Muazu Saadu Kudan Malami a jami’ar kafin Hausa dake Jigawa ya wallafa,

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a Reply