Ƙungiyoyin ma’aikatan jami’a na SSANU da NASU sun janye yajin aiki

0
596

Ƙungiyoyin ma’aikata biyu na jami’o’in gwamnati a Najeriya sun janye yajin aikin da suke yi bayan sun gana da Ministan Ilimi Adamu Adamu a yau Asabar.

Kwamatin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin Senior Staff Association of Nigerian Universities da Non-Academic Staff Union of Educational and Allied Institutions suka kafa ne ya gana da ministan a Abuja.

Sai dai azuzuwan jami’o’in gwamnatin za su ci gaba da kasancewa a rufe saboda ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU ba ta janye nata yajin ba wanda ta shafe fiye da wata biyar tana yi.
Ƙungiyoyin biyu sun fara nasu yajin aikin a watan Maris jim kadan bayan ASUU ta fara nata.

Shugaban ƙungiyar SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim, ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa sun jingine yajin aikin ne tsawon wata biyu da zimmar bai wa gwamnatin tarayya damar aiwatar da alƙawuran da ta yi musu.

Leave a Reply