Ƙasar Birtaniya ta wallafa sunayen yan Najeriya da suka mutu suka bar ɗinbin dukiya a bankunan Ƙasar ba magada

0
474

Daga Fatima MONJA Abuja

Gwammatin ƙasar Birtaniya ta wallafa sunayen yan Nigeriya 56 da suka mutu suka bar tarin dukiya babu shaidan makusanta da za su gaji wannan dukiya.

Jaridar Business day da ake wallafawa a ƙasar tace daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wanda a ƙarƙashin dokokin birtaniya, matuƙar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar da me ita ya mutu matuƙar ba a gano makusantan mamaci ba, to dukiyar ta zama na baitil-mali.

Gwammatin Birtaniya ta wallafa sunayen wasu daga cikin mutanen da suka mutu, ciki har da wani mai suna Mark N’woko da ya rasu tun ranar 9 ga watan disamba 1992 a garin Surrey da ke Birtaniya.

Hakazalika akwai wani mai suna Victor Adefafo Olafemi Fani-kayode wanda ya mutu a ranar 15 ga watan Agustan 2001 a Beimingham, sai dai har yanzu ba wanda ya gabatar da kanshi a matsayin ɗan uwa ko makusanci domin ya gajeshi.

Leave a Reply