Shugaban ƙungiyar addinin musulunci ta Izalatul bidi’a waiƙamatus sunna na ƙasa Shaikh Bala Lau ya bada tabbacin cewa malaman ƙungiyar za su cigaba da yiwa jihar Yobe da Najeriya addu’a domin samun zaman lafiya da yalwar arziki.
Shaikh Balalau ya shaida haka ne a lokacin da ya jagoranci mambobin ƙungiyar reshen jihar Yobe inda suka ziyarci gwamnan jihar a Abuja domin taya shi murnar samun lambar yabo.
A nasa ɓangaren gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya buƙaci malamai a ƙasar nan da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ma shugabaninta.Ya ce malaman addini suna da rawar da za su taka wajen tsara tunanin shugabanni, da jama’a da gwamnati domin samun ingantacciyar ƙasa.
“Ku ne masu tunatarwa, da jagorontar jagororin gwamnati da al’umma. “Ya kamata hudubarku da wa’azinku su jagoranci shugabanni wajen bauta wa Allah da kuma inganta walwalar jama’a.
“Ya kamata ku ci gaba da tunatar da shugabanni irin rawar da suke takawa wajen bautar Allah da jama’a. “Kada ku bar shugabanni kan ra’ayoyinsu da hikimarsu wajen gudanar da harkokin ƙasa,” in ji Gwamna Buni.
Tun da farko, Shiek Bala Lau, ya ce ya jagoranci shugabannin ƙungiyar ne ta musulunci reshen jihar Yobe domin taya Gwamna Buni murnar karrama shi da babbar lambar yabo ta ƙasa da aka yi a kwanan nan.
Sheik Lau ya tabbatar wa Buni cewa JIBWIS na goyon bayan gwamnatinsa don samun nasara. “Za mu ci gaba da yi wa jihar Yobe da Najeriya addu’a domin samun dauwamammen zaman lafiya, ci gaba da wadata,” malamin ya tabbatar.
[…] KU KUMA KARANTA:Zamu cigaba da Addu’a ga Yobe da Najeriya don samun zaman Lafiya- Shugaban Izala […]
[…] KU KUMA KARANTA: Zamu cigaba da Addu’a ga Yobe da Najeriya don samun zaman Lafiya- Shugaban Izala […]