Zaben 2023: An Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Gujewa Yin Amfani Da Kananan Yara Yayin Gangamin Siyasa

1
488

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A YAYIN ake shirye-shiryen zaben 2023, gamayyar Kungiyoyin malaman addini, masu fafutukar kare hakkin yara da kuma sarakuna, sun yi kira ga yan siyasa da kada su bari duk wani yaro da yake kasa da shekaru sha takwas ba su halarci gangamin yakin neman zabensu a cikin al’umma.

Fasto yohanna buru, babban mai kula da Cocin Christ Evangelical And Life Intervention Ministry, ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce ya kamata ‘yan siyasa su hana duk wani matashin da bai kai shekaru sha takwas ba shiga duk wani gangamin siyasa da yakin neman zabensu a cikin al’umma, kasuwanni, filin wasa da dai sauran makamancin wurare.

A cewarsa, sun kafa hadakar shugabannin addinai da sarakuna tare da masu rajin kare hakkin yara wadanda za su shawarci duk masu son yin siyasa kan ingantattun hanyoyin inganta dimokuradiyya mai dorewa da shugabanci na gari a kasar.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da ‘yan siyasar Najeriya za su daina amfani da ‘yan daba a lokacin yakin neman zabe da gangamin siyasa, domin su taimaka wajen ganin an kafa gwamnatin dimokaradiyya tare da karfafa kyakyawan shugabanci a kowace gwamnatin dimokuradiyya.

Ya ce “Gwamnatin dimokaradiyya ta fi ta mulkin soja kyau, don haka akwai bukatar a gyarata saboda makomarmu a yanzu da ta shugabannin Najeriya masu zuwa.”

Ya ce, a yayin da ‘yan siyasa ke fara yakin neman zabe a fadin jihohi 36 na Najeriya, akwai bukatar kada su bari duk wanda bai kai shekaru 18 ba ko kananan yara su halarci gangamin su a mafi yawan al’ummomin da za su ziyarta a lokutan yakin neman zabe.

Yayin da yake yi wa daukacin ‘yan takarar fatan samun nasara, ya sake jawo hankalin masu rike da mukaman gargajiya, kungiyar mata, kungiyoyin matasa, dattawan al’umma da kada su bari matasa su kasance cikin duk wani Kamfe na siyasa a fadin kasar nan, Inda ya ce ” Dole ne mu hada hannu tare don kare ‘ya’yanmu tare da karfafa kyakkyawan jagoranci a kowace gwamnatin dimokuradiyya.”

Buru ya yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da ke kokarin inganta mulkin dimokaradiyya da masu kula da al’ummar Najeriya da kuma hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya da su wayar da kan kungiyoyin matasa a kodayaushe kan ‘yancin kada kuri’a tun suna shekara 18.

Hakazalika, shugaban kungiyar iyayen yara na kasa reshen Najeriya, Alhaji haruna danjuma, ya yi kira ga iyaye da su rika sanya ido a kan ‘ya’yansu a kai a kai.

Yayin da yake kira ga kungiyar mata da su yi kokarin shiga yakin fada da shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin al’ummarsu.

Ita ma shugabar gidauniyar kare hakkin mata da kananan yara a Najeriya, Hajiya Ramatu Tijjani ta yi kira ga duk wani mai fafutuka a kasar da ya fara yakin neman zabe na wayar da kan jama’a kan rage cin zarafin mata.

1 COMMENT

Leave a Reply