Zaɓen cike gurbi: Musa ya lashe kujerar Sanatan Yobe ta gabas

0
133

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Musa Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Sanatan Yobe ta Gabas da aka kammala.

Mataimakin shugaban jami’ar tarayya ta Gashua (FUGA), Ibrahim Ahmed Jajere, wanda shi ne jami’in zaɓe na zaɓen, ya bayyana Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan an kammala ƙidaya ƙuri’u a cibiyar tattara ƙuri’u da ke Kwalejin gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic Damaturu) ranar Lahadi.

Jajere ya ce ɗan takarar jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u dubu 68,778 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Aji Kolomi na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u dubu 18,878.

Jami’in zaɓen ya bayyana cewa, jimillar ƙuri’u dubu 90,949 da aka kaɗa, ƙuri’u dubu 88,771 yayin da ƙuri’u dubu 2,178 suka ɓaci.

KU KUMA KARANTA: Ɗan takarar Sanatan APC a Yobe ta gabas, ya yiwa al’ummomin Geidam da Yunusari alƙawarin morar romon dimokuraɗiyya 

“Ni, Mataimakin Farfesa Ibrahim Ahmed Jajere a nan na tabbatar da cewa ni ne Jami’in zaɓe na cike gurbi na takarar neman kujerar Sanatan Yobe ta Gabas na 2024 da aka gudanar a ranar 3 ga Fabrairu.

“An fafata tsakanin Musa Mustapha na APC ya samu ƙuri’u 68,778, Aji Kolomi na PDP ya samu ƙuri’u 18,878.

“Musa Mustapha na APC bayan ya cika dukkan sharuɗɗan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya dawo zaɓaɓɓe,” in ji shi.

Mustapha wanda aka fi sani da Coolers tsohon kwamishinan kuɗi, sufuri da makamashi ne a jihar Yobe ya maye gurbin Sanata Ibrahim Geidam wanda ke riƙe da muƙamin ministan harkokin ‘yan sanda.

Ga sakamakon kamar haka;

Bursari
APC-9,466
PDP-2,752

Damaturu
APC: 11,941
PDP-6,693

Geidam
APC-6,621
PDP-2,310

Gujba
APC-11,529
PDP-3,037

Gulani
APC-12,516
PDP-2,198

Tarmuwa
APC-5,557
PDP-1,054

Yunusari
APC-11,148
PDP-834

Neptune Prime

Leave a Reply