‘Yar Kaduna ta lashe gasar lissafi ta ƙasa da ƙasa

Wata hazikar yarinya ‘yar Najeriya mai shekaru 13, Nasara James Dabo, ta samu nasarar a gasar lissafi ta ‘yan wasan Olympics na ƙasa-da-ƙasa (IMO) bayan ta cin ye tambayoyin lissafi 34 a cikin kasa da mintuna 3.

Nasara James Dabo ‘yar asalin jihar Kaduna kuma dalibar Ideal International College Kaduna, ta kai matakin karshe a matsayin ɗaya daga cikin matasa a wajen taron bayan ta nuna ƙwazon da ta yi a fannin lissafi.

KU KUMA KARANTA:‘Yar shekara 10 ta lashe gasar haɗa baƙi ta ‘Spelling Bee’ a Borno

A cewar kafar yaɗa labarai ta Liner, hazikar yarinyar, ta kammala fafatawar a gasar da maki 145, inda ta amsa tambayoyin lissafi 34 a cikin daƙiƙa 172 wato a ƙasa da mintuna uku.

Ta fito a matsayin wanda ta fi kowa cin gasar, inda ta doke sama da mutane 150 da aka zaɓa a cikin gasar ta mataki na yara “Junior Category”, a matsayin matsayi na farko na Gmgasar ta Olympiad.

An karrama ta ne da lambar zinare saboda bajintar da ta yi, da kuma sadaukar da kai ga karatun lissafi.

Gasar International Mathematical Olympiad (IMO), gasar lissafi ce ga ɗaliban makarantar sakandare inda ɗalibai ke fafatawa a cikin abubuwan da ke gwada ilimin su na algebra pre-calculus.


Comments

One response to “‘Yar Kaduna ta lashe gasar lissafi ta ƙasa da ƙasa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yar Kaduna ta lashe gasar lissafi ta ƙasa da ƙasa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *