‘Yan ta’adda sun yi wa Birget din Shugaban ƙasa kwanton ɓauna a Abuja, tare da zagaye makarantar koyon aikin lauya

0
395

‘Yan ta’addan da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja na ƙara samun ƙwarin gwiwa, domin kuwa har hari suka kaima jami’an tsaro.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa an kaima sojojin na Elite Guards Brigade hari, waɗanda aikinsu na farko shi ne gadin babban birnin tarayyar Abuja, musamman fadar shugaban ƙasa. Anyi musu kwanton ɓauna a kan hanyar Bwari zuwa Kubwa.

Sojojin sun kasance suna sintiri na yau da kullun a yankin lokacin da aka kai musu hari. Wannan kwanton ɓaunar dai na ƙara tabbatar da fargabar da ake tacewa ‘yan ta’addan suna kewaye a a yankin Bwari da ke ɗauke da makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya, da kuma hedikwatar hukumar ta JAMB.

A taƙaice dai, wata majiya ta lura cewa wataƙila suna shirin kai hare-hare a Makarantar Shari’a da sauran muhimman wurare a yankin.

A halin da ake ciki kuma, dakarun Brigade sun daƙile harin kwantan baunar da ƙarfi. Sai dai sojoji uku sun jikkata a harin, kuma tuni aka kai su jinya a wani asibitin sojoji da ke Abuja.

Cikakkun bayanai kan raunin da sojojin suka samu har yanzu be fito ba. Harin kwanton bauna da aka kai a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna cikin yankin ne kuma mai yiyuwa ne su aiwatar da shirinsu na kai hari a makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya.

Leave a Reply