’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari shingen binciken ’yan sanda da ke ƙauyen Tazame a Jihar Zamfara, inda suka harbe ɗan sanda ɗaya har lahira tare da raunata wasu.

Shingen na da nisan kilomita daya zuwa garin Kwatarkwashi, wanda ke kusa da Gusau, babban birnin jihar.

Majiyoyi da dama sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sama da 40, tare da bude wa shingen wuta da misalin karfe 4 na safiyar ranar Lahadi.

Majiyar ta ce maharan sun kuma banka wa shingen wuta tare da ƙone komai kafin daga bisani suka tsere zuwa daji.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe sojojin Nijar huɗu a kusa da iyakar Najeriya

“’Yan bindigar sun yi wa ’yan sandan da ke wurin yawa inda suka dinga musayar wuta na tsawon lokaci.

“Na samu labarin cewa sauran ’yan sandan sun tsere domin ceton rayukansu. Maharan sun fi ‘yan sanda yawa. An yi sa’a wasu daga cikin ‘yan sandan sun tsere da dukkaninsu za su hallaka.”

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, domin jin ta bakinsa, ya ci tura, domin bai amsa ƙiran da aka masa ba.

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Arewa da ke ci gaba da fuskantar ƙazaman hare-haren ta’addancin ’yan bindiga.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *