Yadda uwargida takaima babbar ƙawarta hari, don ta auri mijinta

Wata uwargida ta ƙasa danne kishin ta, ta kai wa babbar ƙawarta duka saboda ta aure mata mijinta.

A lokacin kammala bikin, sabuwar amaryar ta je ta gai da uwargidan kamar yadda akeyi a al’adance, kuma ana sa ran uwargidan za ta taryeta cikin maraba, kwatsam, sai ta kasa danne fushinta, ta kai mata hari a cikin taron jama’a ‘yan kai amarya.

Bidiyon dake zagaye a yanar gizo ya ɗauko hoton lokacin da matar ta kai wa babbar ƙawarta ta hari.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtube.com/shorts/nUtRnvMjGzw?feature=share

Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa takaici biyu ne ke damun uwargidan, na cin amana da qawarta ta mata, da kuma yadda ta zauna da mijinta cikin talauci, ta tallafawa masa da dukiyar da ta gada na tsawon shekaru, da wannan jarin kasuwancinsa Ya haɓaka yayi arziki, amma ya saka mata da auren aminiyarta.

Saboda hakane, matar farko ta kasa danne fushinta a wajen bikin aure, lokacin da sabuwar matar ta zo gaidata, ta far mata a cikin taron.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *