Labarin yana gefen ku!

Yadda sojan da yayi tatil da barasa ya kashe Janar ɗin sojin Najeriya

1

Wani soja mai muƙamin kofur da yayi maƙil da barasa ya kaɗe janar na sojin Najeriya da mota lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sa.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na ranar Talata a daidai lokacin da marigayin, Birgediya Janar James ke kan hanyar tafiya gidansa da ke cikin barikin sake tsugunar da tsoffin soji ta NAFRC a Legas.

Babban hafsan sojin ya rasu ne a daren ranar Talata sakamakon raunukan da ya samu bayan da kofur Abayomi Ebun da ake kyautata zaton yayi tatul da barasa ya kuma bugu inda ya yi ta tuƙin ganganci a cikin barikin har ya buge shi da mota, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka faɗa wa manema labarai.

Kofur Abayomi Ebun da ake zargi da kaɗe Janar James

An garzaya da Janar ɗin zuwa cibiyar kula da lafiya ta barikin NAFRC bayan faruwar lamarin inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Tuni dai aka kama kofur ɗin da sojan, ana kuma tsare da shi a hannun provost marshals na barikin NAFRC da ke binciken lamarin. Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba a kan lamarin.

Kakakin Rundunar, Onyema Nwachukwu, Birgediya-Janar, bai amsa ba saƙo ba, kuma har yanzu bai amsa kiran da aka yi masa ba domin neman karin bayani. Har ya zuwa rasuwarsa, Birgediya Janar James ya kasance babban jami’in hukumar kuɗi ta sojojin Najeriya. Ya yi digirin farko da na biyu a fannin Accounting da kuma wani ƙarin digiri na biyu a fannin kasuwanci da gudanarwar kuɗi.

Ya kasance ɗan ƙungiyar Akantoci ta ƙasa (ANAN) kuma memba ne a cibiyar gudanarwa ta Najeriya (NIM), cibiyar daraktoci ta Najeriya (MIoD), cibiyar araji ta Chartered (ACTI), da cibiyar ƙasa (mni).

Sannan An yi masa ado da Tauraron Sabis na Meritorious (MSS) da Kwalejin Ma’aikata ta Pass (PSC).

Motar da sojan ya kaɗe Janar James da ita.



Cibiyar sake tsugunar da Sojojin Najeriya da Birgediya Janar James ya yi aiki har zuwa rasuwarsa, wata cibiya ce ta wacce ke dauke da horar da jami’an soji da koya masu ko kuma aikin dogara da kai kafin lokacin yin ritaya daga aikin soji domin su sake da farar hula.

Manufar Cibiyar, in ji hedkwatar tsaro, ita ce a taimaka wa jami’an soji da suka yi ritaya a cikin sauƙi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.