Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Sokoto
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce jam’iyyar PDP ce ta lashe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Sokoto.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Sokoto ya gabatar da sakamakon zaɓen a zauren karɓa da bayyana sakamakon a Abuja
Ga yadda kowacce jam’iyya ta samu ƙuri’u a zaɓen kamar haka:
APC – 285,444
LP – 6,568
NNPP – 1,300
PDP – 288,679
Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar zamfara
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Zamfara ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa;
Ya karanto sakamakon da manyan jami’iyyun suka samu kamar haka:
PDP – 193,978
APC – 298,396
LP – 1,660
NNPP – 4,044
Atiku ya lashe za ben shugaban ƙasa na jihar Kebbi
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Kebbi ya gabatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar a zauren karɓa da tattara sakamakon shugaban ƙasa
Jumullar wadanda aka yi wa rijista 2,032,041
Yawan wadanda aka tantance 599,201
Abin da manyan ‘yan takara suka samu
PDP – 285,175
APC – 248,088
LP – 10,682
NNPP – 5,038
[…] KU KUMA KARANTA:Yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ya kasance a jihohin Sokoto, Kebbi, da Zamfara […]