Yadda rago ya ɓace a motar haya daga Bauchi zuwa Kano

0
174

Mamaki da al’ajabi ne ya kama al’umma a tashar mota ta Gidan Mangwaro da ke titin Ibrahim Taiwo a jihar Kano bayan da wani direban mota da aka loda masa rago daga garin Bulkachuwa na jihar Bauchi, ya neme shi sama ko ƙasa ba a ganshi ba bayan ya isa tashar.

Rahma Radio ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a jiya Juma’a bayan da direban motar ya ɗauki wani fasinja tare da ragonsa da tinkiya daga Bulkachuwa zuwa Kano.

A cewar direban, ya loda ragon da tunkiyar a bud ɗin motar, inda ya tabbatar da cewa tun daga Bulkachuwa, har zuwa tashar Gidan Mangwaro babu inda aka tsaya har ta kai ga an buɗe bud ɗin motar.

Ya ƙara da cewa, amma ko da motar ta isa tashar, an buɗe bud domin sauke kayayyakin da aka loda, sai aka nemi ragon nan sama da ƙasa ba a gani shi ba, sai tunkiyar a zaune ta yi tsuru -tsuru tana ta tiƙa da baki kamar yadda aka ajiye ta lokacin da za a taso daga Bulkachuwa.

KU KUMA KARANTA:Abubuwan al’ajabi da ke tattare da dabbar ‘Batoyi’ (Hotuna)

Gidan rediyon ya rawaito cewa nan dai al’ajabi ya mamaye tashar, inda kan ka ce kwabo, wajen ya cika maƙil da jama’a da su ka yi jugum-jugum suna al’ajabi.

Direban motar ya rantse cewa tun daga tashar Bulkachuwa har zuwa Gidan Mangwaro babu inda aka tsaya har ta kai ga an buɗe bud ɗin motar, ballantana ma ragon ya kufce ya gudu.

Sai dai kuma jama’a da dama na zargin cewa ragon na aljanu ne.

Direban ya ƙara da cewa mai ragon, da fari ya ƙi yarda, inda ya dage sai an biya shi ragonsa, amma daga bisani, bayan shugabancin tashar ya shiga maganar, sai ya ɗauki ƙaddara.

Leave a Reply