Yadda miji ya guji matarsa saboda gemu ya fito a fuskarta

0
257

Wani magidanci yayi watsi da matarsa saboda gashi ya fito mata a haɓarta.

Mandeep Kaur ta yi aure ne a shekara ta 2012 kuma ta yi imanin cewa ta sami abokin rayuwa na har abada.

Shikam mijin Kaur tsaf ya guje wa matarsa a daidai lokacin da ta fara gashin gemu a fuska, kammaninta ya fara sauyawa izuwa irin na maza, inda ya watsar da aurensu cikin ‘yan shekaru.

KU KUMA KARANTA:Dalilai 7 masu Haɗari da zai sa mu guji cin gandar fatar dabbobi

Matar mai shekaru 33 ta shiga tashin hankali bayan aurenta ya mutu, ta ji kamar rayuwarta tazo ƙarshe saboda wannan cutar halitta da ke kira Hirsutism.

Menene hirsutism?

A cewar wani masani ta fuskar lafiya Mayo, hirsutism wani yanayi ne a cikin mata wanda ke haifar da tsayi da yawa na gashin a cikin fuska, ƙirji da baya.

A cutar hirsutism, ƙarin gashi yakan taso daga haddi na hormones na maza (androgens) testosterone.

An ba da rahoton cewa Kaur taƙi karbar lalurar, amma daga baya, ta yanke shawarar neman taimako, inda ta fara halartar Gurdwara – wurin ibadar mabiya addinin Sikh.

Kuma a hankali Kaur ta rungumi ƙaddararta, ta bar gemunta. Ta ke ɗaura rawani, ta dena aske gemunta da gashin baki.

Takan hau babur ta zagaya ƙauyensu tana noma tare da yayyenta, wani lokaci mutane kan yi mata kallon namiji, amma muryarta na tona mata asiri cewa mace.

Ta ce ta ɗauki lokaci kafin ta saduda, amma a ƙarshe ta haqura, don haka ta daina jin kunyar gemun nata.

Leave a Reply