Yadda BBC ta rasa ƙwararrun ma’aikatanta tara da suka koma TRT

2
666

Daga Saleh Inuwa Kano

Akalla ‘yan jarida tara na Sashen Hausa na BBC a Najeriya sun yi murabus a cikin wata ɗaya da ya gabata, a wani abin da aka bayyana a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kafafen yaɗa labarai na duniya.

Aminiya ta gano cewa ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da manyan ‘yan jarida guda biyu, ’yan jarida uku na kafafen sada zumunta – biyu daga cikinsu manyan ‘yan jarida ne – babban mai ba da rahotannin harsuna biyu na Hausa/English Africa, mai ba da rahotannin kafafen yaɗa labarai da kuma ‘yan jaridar bidiyo guda biyu.

KU KUMA KARANTA:Zamu fi aminta da ‘Yan China su koya mana noman shinkafa maimako su noma ta a Yobe, ra’ayin jaridar kore shakku

An tattaro cewa yayin da biyar daga cikin ‘yan jaridar suka bar watan Disambar da ya gabata; Sauran huɗun sun yi murabus ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata don shiga sabon sashen Afirka na Rediyo da Talabijin na Turkiyya (TRT) a Istanbul.

“Wannan ba irinsa ba ne a tarihin BBC Hausa. Wasu ‘yan jarida tara na BBC Hausa sun shiga cikin shirin da za a fara aiki da shi nan ba da dadewa ba bayan da gwamnatin Turkiyya ta yanke shawarar kafa TRT Africa: Hausa, Swahili, French and English for Africa,”
kamar yadda wata majiya ta BBC ta shaida wa wakilinmu.

Majiyar ta ce Nasidi Adamu Yahaya, wanda ya yi murabus daga matsayin babban ɗan jarida na zamani, zai jagoranci sashen Hausa na TRT, tare da wasu manyan ‘yan jarida, Halima Umar Saleh da Ishaq Khalid a matsayin mataimakansa.

Da aka tambayi ɗaya daga cikin ‘yan jaridan da ya nemi a sakaya sunansa, da aka tambaye shi ko me ya kai ga yin murabus fin da yawa, ya ce an ɗauki matakin ne kan yadda kafafen yaɗa labarai na Turkiyya suka kuduri aniyar bayar da labarai masu kyau a Afirka.

2 COMMENTS

Leave a Reply