Zamu fi aminta da ‘Yan China su koya mana noman shinkafa maimako su noma ta a Yobe, ra’ayin jaridar kore shakku

2
327

A ranar 20 ga wata Yuli ne, fadar Gwamnatin Jihar Yobe ta fitar da labarin cewa wasu gungun manoma ‘yan ƙasar China ƙarƙashin jagoransu Mista Yung Wang na shirin kwararowa jihar Yobe domin  neman filin noman shinkafa har kadada da ta kai hekta dubu goma.

Kodayake, da yawan mutane na ganin haka a matsayin ci gaba amma masana tun da daɗewa sun zaburar da al’ummar ƙasashen Afirka cewa nahiyar na iya zama wuraren da baƙi fararen fata da za su zo da su mamaye filayen noma da al’uma ke da su tare da kuma maida al’umar leburorinsu da ba za su amfanu ba da abin da ake nomawa daga filayen da fararen fatar suka mamaye.

Mun san yadda tsarin dokokinmu suke da rauni kan sha’ani da ya danganci harkar filaye musamman in har al’amari ya shafi harka da manyan kamfanoni da a turance ake kira corporate accumulation of land. A ƙasashe kamar Zimbabwe, da Afirka ta Kudu, da Namibiya, da Congo da kuma Kamaru a baya-bayan nan, fare-fare fata masu ƙarfin tattalin arziki sun yi sanɗa cikin wayo suka mamaye filayen noma tare da maida masu filaye bayinsu. Al’amari da ya kai har ya rikiɗe ya koma mulkin mallaka a  ƙasashe kamar Zimbabwe, da Afirka ta Kudu, da Namibiya.

Bisa cewar Bahaushe, gani daga wani ya ishi wani ji tsoron Allah, ina kira da mahukunta da su yi kaffa-kaffa a duk lamari da za a yi baƙi ‘yan  ƙasashen waje kan al’amari da ya danganci filin noma don kar a mana sakiyar da ba ruwa mu da jikokinmu.

Ya kamata a yi amfani ƙwararu lauyoyi da muke da su wajen shata yarjejeniya da irin waɗannan mutane ta yadda ba mallake mana filaye za su yi ba sai dai kawo mana fasahar da za ta inganta mana nomanmu.

Wannan ra’ayi ne na Jaridar Kore Shakku ba muzantawa ba ne.

2 COMMENTS

Leave a Reply