Yadda aka min dukan mutuwa ina tsaka da ɗaukan rohoton ambaliyar ruwa a Ganuwar Kuka.

1
747

Daga Abubakar TAHIR, Hadejia

Labarin cike yake da ban tausayi, dalilin rashin gaggauta ɗaukan matakin gaggawa daga mahukunta kan lamarin ambaliyar ruwa dayake cima mutane tuwo a kwarya tsawon shekaru babu kuma wani shiri na musamman daga gwamnatoci wajen daƙile wannan matsalar.

Dayake lamarin ambaliya ya ƙazanta a garin Hadejia dama garuruwa kamar Ganuwar Kuka, Auyo, Hago, Kadime, Kubayau dss. Wannan tasa gidajen radio da jaridu suka rinƙa tuntuɓata domin sanin halin da kuma matakin da gwamnati ke ɗauka kai tsaye.

Bayan shigata garin Ganuwar Kuka, na lura da cewa cikin mintuna sha biyar ruwa ya kusa gamawa da garin. A take na gabatar da ID Card ɗina na aiki inda wasu matasa danakega sun waye suka biyo ni domin yin hirasa dasu.

Bayan na ɗora musu kyamara don na naɗi abun da suke da bukata haka tasa matasan suka faɗi irin halin da suke ciki tare da neman agajin ƙungiyoyi. Bayan mun kammala na ɗan gusa gaba kaɗan domin cigaba da daukan bayanai.

Katsam sai naji an taho da gudu inda aka bugeni da ƙarfi a kaina, a take wayoyin dake hannuna ƙirar Infinix da Itel suka zuge cikin ruwa. Ɗagowar da zanyi domin naga wanne dalili sai naji an cigaba da dukana ta koina aka dannan kaina cikin wani rafi da suke Kira ruwan Makasa. A haka sukayi ta dilmiya kaina suna dukana wasu suna cewa ku dake shi Nikwa inata kokarin nusar dasu ID card dina ina ce musu aiki nake.

Bayan Ɗan wani lokaci na fiddar rai daga cigaba da nunfashi nan take wasu mutane sukayi ta maza suka hanasu wanda daba dan an kawomin ɗaukin ba da tuni sun kasheni tunda a take wasu sun zare wuqaqe.
Wasu suna ku kasheshi, ɓarawone, Ina ce musu kuduba ID card dina.

Haka aka kaini gidan Maigari ya bani ruwa nayi wanka ya bani sabin Kaya na saka Inda ya buƙaci na dawo na cigaba da aiki nace masa A’a. Najefar da kuɗaɗena inda aka kawomin ɗan abinda yarage naira 2500.

A haka Maigari Ya bada babura aka kawoni Haɗejia inda a take na tafi babban asibitin Hadejia domin jinya. Na ɗauki tsawon kwanaki uku a asibitin banma san a Ina nake ba. An sallameni ranar juma’a zuwa gida domin cigaba da karɓan magani.

Abokanen aiki Yan jaridu sun ji halin da nake ciki inda labarin ya chanja daga jin halin danake ciki.

Mutanen Garin sun buƙaci a cigaba da kawo musu ɗaukin tare da SAWABA Fm, suna nuna rashin jin ɗadinsu Kan abinda ya faru dani. Ya zuwa yanzu jikina na daɗa samun sauƙi, saidai Ina fama da matsananci ciwon wuya da baya sakamakon harin.

Haka Kuma na sanar da jamian tsaron farin kaya,Yan sanda, Civil defence, Ƙungiyar Yan jaridu, domin zaƙulo waɗannan ɓatagari wanda suka yi ƙoƙarin hallakani, Allah yayi da sauran kwana a gaba.

Jamian tsaro sun gayyaci Mai garin inda ya tabbatar da faruwar lamarin Wanda yake da alaqa da sakacin gwamnati wajen shigowa cikin lamarin ambaliyar, wanda suka huce haushinsu a kaina danaje ɗaukan rohoton.

Haka shima Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Baffa shinge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya zuwa yanzu dai, jami’an tsaro na ciga da bincike wajen ganosu inda ni
kuma nake cigaba da jinyar harin, nake sa rai kan samun adalci daga garesu.

1 COMMENT

Leave a Reply