Kampanin Apopo na ƙasar Belgium ya horar da wasu haziƙan ɓeraye domin yin aikin ceto ga waɗanda ɓaraguzan girgizar ƙasa suka danne har yau ba a gano su ba.
“Anyi amfani da ɓeraye ne saboda a yanayin tsarin halittar su, suna da sha’awar sanin abu, da kuma son kutsa kai da bincike, wannan dalili yasa aka gane tsaf zasu iya taimakawa wajen ceto,” in ji Donna Kean, ƙwararren masanin kimiyyar ɗabi’a kuma shugaba mai jagorarantar aikin.

“Banda ɗabi’ar ɓera na binkice da shige shige, ƙanƙantar halittar su, da baiwar jin ƙamshin da wari koda daga nesa, ya beraye suka zama mafi chanchanta don yiwa duniya wannan aiki”, in ji Kean.
KU KUMA KARANTA: Allah ɗaya gari bam bam! Gizo-Gizo, abincin yau da kullum a Kambodiya
An sanyawa ɓerayen wata babbar jaka da take ɗauke da na’urar GPS ta zamani da kyamarar ɗaukar hoto mai inganci, da kuma makirufon.
Haka kuma akwai wata na’urar wayar salula da za a iya magana da mutanen da suka maƙale amma ba su kai ga rasa rayukansu ba.

Sannan za a iya ganin mutumin da abin ya rutsa da shi, gami da gane irin yanayin da yake ciki, sannan a gano hanya mafi sauƙi da za a iya ceto shi a fito da shi.
Wannan ya zama izina garemu mutane, idan har ɓera yana kishin ƙasarsa, yana bada gudunmawa mai mahimmanci wajen cigaban ƙasa, ya kamata mu tambayi kanmu, mu wane gudunmawa muke bawa ƙasar mu domin cigaban ta, a matsayin mu na yan Adam.