Wata budurwa ta faɗi, ta mutu a cikin rijiya a Kwara

1
281

Wata budurwa ‘yar shekara 21 mai suna Hamudat ta faɗa cikin wata rijiyar gida da ke Ilorin babban birnin jihar Kwara a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda aka tsinci gawar ta.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa matar na da taɓin hankali.

Lamarin mai ban tausayi ya faru ne a harabar Ile-Kangu, yankin Pakata a cikin babban birnin Ilorin a ƙaramar hukumar Ilorin ta yamma.

Hukumar kashe gobara ta jihar, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce mummunan lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 14:55 (02:55 na rana).

KU KUMA KARANTA: Wata mata ta mutu a rijiya, a lokacin da ta take ɗiban ruwa a Kwara

A cewar shugaban sashen, yaɗa labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Hassan Adekunle, ‘yan kwana-kwana da suka ƙwato mamaciyar sun miƙa gawar ta ga mahaifinta, Alhaji Suleiman Issa.

“Saboda haka, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya yi amfani da wannan damar wajen baiwa jama’a shawara da su ba da fifiko ga tsaro da kuma kula da harkokinsu na yau da kullum.

Haka kuma su dena tura yara masu ƙarancin shekaru zuwa ɗiban ruwa a rijiyoyi”.

1 COMMENT

Leave a Reply