Kungiyar ‘yan sintiri So-Safe Corps ta kama wani matashi mai shekaru 24 a otal bisa zarginsa da yunkurin kwashe wasu kaya masu daraja a ɗakin da ya kama a wani otal jihar Ogun.
Wanda ake zargin, mai suna Muhammad Abubakar, ya je Otel ɗin ne tare da budurwarsa inda ya ɓuge da sace kayayyakin da suka haɗarda fankoki, ƙwayaƙwayai da sauransu.
Rundunar ‘yan sintirin ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fito daga ofishin kwamandanta na jihar Ogun Soji Ganzallo, ta hannun daraktan yaɗa labaranta da hulɗa da jama’a, ACC Moruf Yusuf, sanarwar ta ce, wanda ake zargin ya yi nasarar katse wasu na’urorin lantarki tare da cire wasu kayayyaki masu daraja a lokacin da aka gano shi.
KU KUMA KARANTA:Wuta ta kama wani mutum lokacin da yake tsaka da satar waya a taransfoma
Wanda ake zargin Abubakar, mazaunin unguwar Oloko ne a Otta, an ce ya je otal ɗin mai suna Keke da ke Iyana-Iyesi, shi a garin Otta, tare da wata budurwarsa da misalin karfe 11:00 na dare a ranar 5 ga watan Janairu, 2023, inda ya kama ɗaki a Otel ɗin.
Ganzallo ya bayyana cewa, an ruwaito matar ta nufi babbar kofar otal din, a yunƙurinta na ficewa daga otal din, amma wani ma’aikacin Otel ɗin ya mayar da ita, dalili kuwa, ba za ta iya fita ba sai da mutumin da ta zo tare da shi.
Domin ya tabbatar ba wata matsala, sai ma’aikacin ya koma ɗaki tare da wannan matar, kuma abun da ya gani ne ya gigita shi, bayan da ya ga Abubakar ya kwance kebul na kamarar CCTV, ya kwance fankan silin da sauran kayayyaki masu daraja a dakin.
“Nan da nan rundunar ta samu labarin cewa, wani wanda ya kama ɗaki a otal ɗin yana nuna rashin da’a, sai tawagar rundunar ta musamman a sabuwar rundunar da aka kirkiro a yankin Ilogbo, ƙarƙashin ACC Idris Odukunle da mataimakinsa, CSC Yusuf Samuel, suka zage damtse domin ƙara ƙaimi da kuma tabbatar da cewa an kama mai laifin,” in ji Kwamandan Rundunar.
Ganzallo ya bayyana cewa, “A lokacin da tawagar ta isa otal din, an gano cewa wanda ake zargin ya watse tare da lalata ɗakunan otal guda biyu, duk da cewa ya bijire wa kama shi, ya cije yatsa na ɗaya daga cikin jami’an.
“Daga ƙarshe dai an damke shi, aka kama shi da misalin karfe 1:00 na ranar Juma’a, 6 ga watan Janairun 2023, kuma an tura shi ofishin ‘yan sanda na Onipanu, tare da abubuwan da aka kama shi ya ɗauka, domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi gaban kotu” in ji Ganzallo.
[…] KU KUMA KARANTA:Wani matashi da yaje Otal da budurwarsa ya ɓuge da sace kayan otal su […]