Wuta ta kama wani mutum lokacin da yake tsaka da satar waya a taransfoma

2
286

Wani matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Ezekiel ya samu rauni a lokacin da yake kokarin satar wata wayar wuta, a yankin Utako da ke babban birnin tarayya a ranar Asabar da daddare.

Wani direban mota ne, ya bayyana cewa Ezekiel ya samu munanan ƙuna bayan da wutar lantarki ta ja shi.

“Wani mutum da aka fi sani da Ezekiel,ya samu rauni bayan wutar lantarki ta kama shi.

“Ya so ya saci waya daga babban taransfoma, na kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja kuma ana cikin haka ne wutar lantarki ta kama shi.

“Mun ji karar tartsatsin wutar lantarki a cikin dare kuma mun ji kururuwar mutumin.

KU KUMA KARANTA:Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta

“Da bamu ga zarto, da filaya, da tocila da suka watse a ƙasa ba, da mun yi tunanin yana son kashe kansa.
Amma kayayyakin aikin da ya tafi da su ne yasa muka gano manufarsa.

Mutumin ya yi sa’a bai mutu ba, amma ya samu raunuka da dama na kuna.” direban yace.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Jami’an mu a lokacin da suke sintiri sun haɗu da shi; ya samu munanan ƙuna, inda suka garzaya da shi babban asibitin Wuse inda ya ke jinya a yanzu, babu shakka za a tuhume shi amma za mu jira har sai ya warke sarai. Kayan aikin sa na hannunmu.” inji ta.

2 COMMENTS

Leave a Reply