Wani zakaran dara na wasan ‘Chess’ ɗan Najeriya kuma mai fafutukar koyar da ilimin yara yana ƙoƙarin buga dara na tsawon sa’o’i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin ‘Times Square’ na birnin ‘New York’ domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi daɗewa.
Tunde Onakoya, mai shekaru 29, yana fatan tara kuɗi dala miliyan 1 don ilimantar da yara a faɗin Afirka. Yana fafata wasan ne da Shawn Martinez, zakaran chess na Amurka, daidai da ƙa’idojin Guinness World Record cewa wajibi ne ‘yan wasan biyu su yi duk wani ƙoƙari na zarta tarihin da aka kafa, inda za su ci gaba da fafata wasan har na tsawon lokacin.
Onakoya ya buga wasan daran har na tsawon sa’o’i 42 da ƙarfe 10:00 na safe agogon GMT a ranar Juma’a. Goyon baya na ƙaruwa ta yanar gizo da kuma wurin wasan, inda ake jin waƙoƙin Afirka da masu kallo suka sa da magoya baya, suna kuma murna da tafin ƙarfafa ‘yan wasan.
Tarihin mafi tsawon wasan dara na Chess a yanzu shi ne sa’o’i 56, mintuna 9 da daƙiƙa 37, wanda Hallvard Haug Flatebø da Sjur Ferkingstad suka kafa a shekarar 2018, dukkansu daga ƙasar Norway.
Yunƙurin sa na kafa tarihin na da manufar “samarwa miliyoyin yara a faɗin Afirka ilmi waɗanda ilimi ba ya kai wa garesu,” in ji Onakoya, wanda ya kafa ƙungiyar wasan Chess in Slums Africa a cikin 2018. Ƙungiyar na son tallafa wa don ilmantar da aƙalla yara miliyan 1 marasa galihu a faɗin nahiyar.
“Ina da ƙwarin gwiwa ɗari bisa ɗari a yanzu saboda mutanena suna nan suna bani goyon baya da kiɗa,” in ji Onakoya da yammacin Alhamis bayan ‘yan wasan sun haye sa’o’i 24 suna gwabzawa.
KU KUMA KARANTA:‘Yan bijilante sun kashe matashi a kan bashin dubu bakwai
A batun abinci na Onakoya, yana shan ruwa da yawa da shinkafa dafa-duka, ɗaya daga cikin sanannun abincin Yammacin Afirka.
Ga kowace sa’a ta wasan da aka buga, Onakoya da abokin karawarsa suna samun hutun mintuna biyar kacal. Wani lokaci ana haɗa hutun wuri ɗaya, kuma Onakoya yana amfani da su don tattaunawa da ‘yan Najeriya da na New York da ke wurin suna ƙarfafa masa.
An tara dalar Amurka 22,000 a cikin sa’o’i 20 na farko na yunkurin, in ji Taiwo Adeyemi, manajan Onakoya.
“Samun goyon bayan ya kasance mai yawa daga ‘yan Najeriya a Amurka, shugabannin duniya, shahararrun mutane da ɗaruruwan masu wucewa,” in ji shi.