Daga Fatima GIMBA, Abuja
An rawaito cewa, yayi digiri 145 akan fanni daban-daban na ilimi dan har ya samu zama daya daga cikin wadanda suka fi ilimi a duniya kamar yadda bincike ya nuna.
Yana koyar da darussa sama da 100 a kwalejoji daban-daban na ƙasar Indiya.
A wata hira da manema labarai, Farfesa Parthiban yace, “ina jin dadin karatu sosai, bashida wahala ko kadan, tsarin shirye-shiryen jarabawa da neman sabbin digiri ko kwasa-kwasen difloma shine abin da nake jin dadin yi” inji shi.
Jerin kwalayen da kwasa-kwasen digiri da yake da su sun hada da; digiri 8 na masters a sashin Law (Shari’a) (ML), masters 10 a Arts (MA), masters 8 a Commerce degrees (M.Com), masters 3 a bangaren Science degrees (MSc), research degrees (M.Phil) 12, da kuma masters 9 a Business Administration degrees (MBA).