Uwar Bari Ta Sanya Wata Mata Daina Sana’ar Karuwanci Bayan Farkawa Ta Ganta A Makabarta

1
789

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA mata wacce ta ke aikin bin maza ko ta ke zaman kan ta da sunan sana’ar karuwanci, ta sha alwashin daina sana’ar da ta jima tana yi sakamakon wata uwar bari na farkawa ta ganta a cikin tsakiyar Makabarta a kwance da ta yi bayan da ta bi wani mutumi izuwa gidan shi ta kwana da shi.

Matar wacce ta buƙaci sakaya sunan ta na asali, a hirarta da manema labarai, ta bayyana cewa ba ta taba tunanin zata daina aikin Karuwancin ba, domin harka ce da ta ke samun kudi da ita, tun ma ba ace mace tana da kyau da yarinta ba, kana ace ta iya kwalliya da rangwada.

Ta kara da cewa, da wannan sana’ar a dare daya ta kan samu Kudi masu dinbin yawan da hakan kan ba ta damar yin yadda ta ke so da cin abin da ta ke so, da sanya tufafi irin wanda ta ke son sakawa a jikinta, amma zancen saurayi ko soyayya ba ta san wannan ba saboda ba ta taba yi ba.

Acewarta, sai dai daga baya da wannan al’amarin ya faru, kwasam babu shiri ta yi rantsuwar ba ta ba wannan harkar na karuwanci, kuma ta ke yiwa sauran Mata masu yi ma fatan Allah Yasa su daina ba tare da sun ga wata ishara ba.

Ta ce “Wata ranar asabar na fito kamar yadda na saba ina kai goro ina kai mari a inda muke tsayawa maza suke zuwa su dauke mu, domin yin farautar kwastoma. Nayi shiga kusan akasarin jikina a waje yake, sai ga wata gingimemiyar mota ta tsaya a gabana, bayan na leka ne ya nuna na masa yana son na bishi gidansa mu kwana.”

“A tsarina bana bin mutumin da bansan shi ba gidansa, amma saboda kyaun mutumin nan ko musu haka ban masa ba kuma cikin girmamawa ya fada mun abin da zai bani wanda kudi ne masu tsoka da ya kamata idan na same su ace na daina karuwanci. Amma ni a wannan lokacin ba kudin bane a gabana kawai na kamu da son shi ne nan take.”

“Ya kaini shagon sayayya na sayi abin da nake so naci, muka kama hanyar zuwa gidansa. Wani katafaren gidane mai matukar kyau da kyalekyele. Muna dosan gidan na tsorata har sai daya gane, kuma nan take yace mini kada na damu bazai cutar dani ba.”

“A takaice, muka kwanta bacci bayan mun gama komai. Wajen karfe 5 na asuba sai nace bari na tashi domin na koma gida kamin gari ya gama wayewa saboda irin wannan shigar danayi.”

“Ai kuwa ina bude idanuwa na sai na ganni a tsakiyar makabarta ina kwance ni kadai. Ga kudi an ajiye mini kusa da jakata. Ga kuma duk kayayyakin dana sayo naci a inda na zauna na ci. A lokacin tsoro ya kamani, na dauki kudin da jakar da kyar na samu hanyar fita.”

“Na kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu kamin na samu kaina da kyar. Wannan yasa nayi alkawarin na daina karuwanci har a bada.”

Wannan dai wani darasi ne na musamman daya kamata mata masu wannan harkar su dauka daga wannan labarin da uwar bari yasa ta rabuwa da aikin ta zubar.

1 COMMENT

Leave a Reply