Tsohon Ministan Wasanni Solomon Dalung Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

0
329

Daga Isah Ahmed, Jos.

TSOHON Ministan wasanni Solomon Dalung ya fice daga Jam’iyyar APC. Tsohon Ministan ya bayyana ficewar tasa daga Jam’iyyar APC ne a wata wasika da ya rubutawa shugabannin Jam’iyyar na Mazabarsa, ta Sabon Gida da ke Karamar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato.

Tsohon Ministan wanda ya yi Ministan wasanni a gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, daga shekara ta 2015 zuwa shekata ta 2019, ya soki gwamnatin Jam’iyyar APC da kasa cikawa al’ummar Najeriya alkawarin da ta daukar masu. Don haka ya ce ya fice daga cikin jam’iyyar.

Leave a Reply