Labarin yana gefen ku!

Tilas mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda – Bola Tinubu

1

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Yinubu ya ce daga yanzu duk wasu masu aikata “ƙazamin” laifi irin na satar mutane don karɓar kuɗin fansa za a ɗauke su a matsayin ƴan ta’adda.

Da yake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na fatattakar ƴan bindiga, shugaban ƙasar ya ce waɗanda ke yin garkuwa da yara matsorata ne da ba za su iya tunkarar ƙarfin sojojin Najeriya ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake buɗa-baki da alƙalan gwamnatin tarayya a ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin Alƙalin-Alƙalai na Najeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

”Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ƴan ta’adda. Su matsorata ne. Wulaƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa ƙarfi.

“Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa. Dole ne mu ɗauke su daidai a matsayin ƴan ta’adda don mu kawar da su, kuma na yi muku alƙawarin za mu kawar da su,” in ji Shugaban Ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Na gaya wa Shugaban Ƙasa matsalolin Zamfara kuma ya ba ni tabbacin kawo ɗauki – Dauda Lawal

Waɗannan kalamai na Tinubu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumomi sun ceto yara ƴan makarantar firamare da aka sace a garin Kuriga na jihar Kaduna mako biyu da suka wuce.

Tun da fari a ranar Talatar, Shugaba Tinubu ya gana da gwamnan jihar Zamfara, inda matsalar satar mutane da fashi da makami suka fi ƙamari, kuma gwamnan ya ce Shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin taimakawa don kawo ƙarshen “bala’in” da jihar ke fama da shi na rashin tsaro.

Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro daban-daban, musamman a jihohin arewacin ƙasar irin su Zamfara da Kaduna da Katsina da Neja da Sokoto.

Sai dai Tinubu ya sha nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa sasantawa da ƴan bindiga ba ko kuma ba su kuɗin fansa.

A hannu guda kuma, Shugaban Ƙasar ya sha alwasin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don inganta yanayin aikin ma’aikatan shari’a a ƙasar.

Kazalika ya gode musu da nuna jin daɗinsa ga ɓangaren shari’a bisa sadaukarwar da suke yi wa ƙasa, inda ya yaba da rawar da suke takawa wajen tabbatar da martabar ɓangaren shari’a na gwamnati.

Leave A Reply

Your email address will not be published.