Tashin gobara a kasuwar waya a Damaturu, an yi asarar dukiya mai yawa

0
74

Daga Ibraheem El-Tafseer

An wayi gari a birnin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe da mummunar gobara wadda ta lanƙwame miliyoyin nairori a babbar kasuwar waya da ke bayan Tasha, a yau Talata.

Babu wanda ya san musabbabin tashin gobarar, kawai dai an ga wuta tana ci, inda ta ƙone shaguna sama da 50 ƙurmus, ɗauke da kayan kuɗaɗe masu ɗimbim yawa.

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya ziyarci kasuwar ya jajanta musu, sannan ya ba da kuɗaɗe masu yawa don rage musu asarar da aka yi. Sannan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) ta ba da naira miliyan uku don rage musu asarar da aka yi.

Xan tarakarar Sanatan Yobe ta Gabas a jam’iyar APC, Alhaji Musa Mustapha ya ba da naira miliyan biyar, don rage musu raɗaɗin asarar da aka yi.

Jama’a da dama ne suke ta zuwa jaje da alhini na wannan ibtila’in gobara wadda ta lanƙwame miliyoyin nairori.

Leave a Reply