An haifi Alhaji Dakta, Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a Cikin shekara ta Alif da Ɗari Tara da Goma Sha Ɗaya (1911), a cikin garin Kagara sa’an nan ta na cikin lardin Kontagora, yanzu kuwa a jihar Neja.
Ya yi makarantar horar wa, wato Katsina Training College, kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekara ta Alif da Ɗari Tara da Talatin da Biyu (1932).
Ya na da shekaru Ashirin da Biyu (22), ya rubuta “Ruwan Bagaja.” Ganin ƙwazonsa wajen ƙaga labari mai ma’ana ya sa Dr. R.M. East, shugaban Ofishin Talifi na Zariya, ya roƙi a bada shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce-rubuce a Zariya.
A zaman sa na Zariya ne Abubakar Imam ya wallafa littafin Magana Jari Ce (1-3), Ikon Allah (Na 1 zuwa Na 5) da Tafiya Mabuɗin Ilimi.
KU KUMA KARANTA:Tarihin Alhaji Abubakar Imam, shahararren marubuci a ƙasar Hausa (kashi na ɗaya)
Nothern Privinces Newsheet ne kamfani na farko da ke buga rubutun ajami a ƙasar Hausa, wadda aka kafa a Kano. Daga baya kuma an kafa Nothern Nigeria Publishing Company (NNPC) waɗanda suke wallafa litttatafai a cikinn Harshen Hausa. Sannan aka kafa gidan jarida ta farko mai suna “Gaskiya Tafi Kwabo” ma’ana; “Truth is Worth More than a Penny” wacce aka ƙirƙira a shekara ta Alif da Ɗari Tara da Talatin da Tara (1939), wadda a lokacin Abubakar Imam shi ne mai kula da harkokin rubutu a kamfanin.
Abubakar Imam ne mutum na farko da ya fara wallafa littafin labarin Hausa a ƙasar Hausa mai suna “Ruwan Bagaja” a shekara ta Alif da Ɗari Tara da Talatin da Huɗu (1934), a lokacin ya na da shekaru Ashirin da Uku (23) a Duniya, sai Bello Kagara, wadda Yaya ne ga Abubakar Imam, wadda ya wallafa littafin Ganɗoki littafi mai shafi Arba’in da Biyar (45).
Sai littafi mai suna “Idon Matambayi” na Muhammadu Gwarzo a shekara ta (1911 zuwa shekara ta 1971). Littafi na biyar shi ne “Jiki Magayi,” amman littafin Magana Jari ce tafi kowanne littafi karɓuwa a ƙarnin.
1- Ruwan Bagaja Abubakar Imam
2- Shaihu Umar Tafawa Ɓalewa
3- Idan Matambayi Muhammadu Gwarzo
4- Ganɗoki Bello Kagara
5- Jiki Magayi John Tafida da Rupert East
6- Magana Jari ce Abubakar Imam
Abuabakar Imam ya ce, ya ɗauke shi kimanin wata shida ya na rubuta littafin Magana Jari Ce. Yawancin labaran da ke cikin littafin Magana Jari Ce ya samo ne daga labarun tatsuniya na Grimon, labarun larabawa da ƴan Indiya kuma kimanin labarai 80 ya samo su daga wasu lttatafan da Rupert East ya ara, shi kanshi Abubakar Imam ya ce, “Shi kanshi Rupert East ya tattaro bayanai daga cikin littatafai daban-daban na turawa da tatsuniyan larabawa, domin yin amfani da su a matsayin abun amfani na sharan fage.”
Magana Jari ce ta kasance babban littafin da tafi kowanne a jadawalin tsarin rubuta littafi ga Hausawa zuwa yau ɗinnan.
RUWAN BAGAJA
Ruwan Bagaja ya na ɗaya daga cikin shahararrun littafin da Abubakar Imam ya wallafa, littafin labari ne a cikin labari, inda Alhaji Imam ke bada tarihin rayuwarsa da kansa. Inda yake tara mutane ya na ba su labarinsa, su kuma su na jinsa.
Labarin littafin ya ƙunshi inda Imam ke barin gida wajen neman Ruwan Bagaja domin neman ma wanda ya riƙe shi Magani da kuma fitar da shi daga kunya. Inda ya fita gida tin da ƙuruciyar shi in da yawo ya kai shi har Indiya, in da daga bisani yake dawowa gida.
Rupert East, ya sanya gasar littattafai, in da aka kai “Ruwan Bagaja” don gyare-gyare a lokacin ta hanyan Katsina Middle School. A watan Aprilu 30th, 1934, Rupert East ya rubutawa Mr. Allen, Shugaban Makarantar Katsina Middle School ga Mallam Abubakar Imam, cewa su na godiya, da turo takardan Abubakar Imam da aka yi zuwa wajen su amma a wannan lokacin baza su iya wallafa littafin ba domin littafin ya ruwaito labarinsa da yawa daga wasu littattafan inda kuma babu wasu canje-canje.
Duk da cewa, littafin ya tsaru kuma sun yabe shi. In da ya ba shi shawarar da ya rubuta wasu labaran da kan shi domin a sanya su, domin samun damar wallafa littafin da sunan shi shi Abubakar Imam.
A watan Agusta. East ya sake rubutawa Abubakar Imam, wasiƙa in da yake sanar da shi cewa, sun kusa gama gyare-gyaren littafin nasa a cikin littafin.
Ya fara nazarin littafin shi wanda ya same suna “RUWAN BAGAJA” a wannan shekarar. In da shekara mai zuwa baturen mulkin mallaka ’Rupert East’ ya sanya gasan littattafai inda aka kai Ruwan Bagaja domin gyare-gyare. Masana Harshen Hausa sun tabbatar da cewar har ya zuwa yanzu babu wani marubuci da ya bai wa Adabin Hausa gudun mowa ta musamman fiye da Alhaji Abubakar Imam, domin kasancewarsa marubuci mai cikakkiyar basira da fasahar shirya labarai iri daban-daban. Duba da muhimmancinsa ne ma, ya sa masana su ka sanya talifinsa cikin jadawalin darussan Hausa a Makarantun Sakandire da kuma Jami’o’i.
Waɗansu littatafan da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta sun haɗa da; Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W) Kammalalle da kuma Ƙaramin Sani Ƙuƙumi. Haƙiƙa, Alhaji Abubakar Imam ya na sahun gaba a manyan taurarin adabin Hausa kuma wadda har ila yau ba shi da tamka a fannin ƙaga Labarai
Nagarta
Duba ga irin gudun mowa da ya bayar ga tallafi da Aikin Jarida, Masarautar Burtaniya ta girmama Alhaji Abubakar Imam da lambar girma ta O.B.E, Order of British Empire. Daga bisani kuma gwamnatin Najeriya ta girmama shi da tata lambar makamanciyar O.B.E, wato C.O.N. Yanzu haka, gwamnatin Jihar Kano ta sanya sunan shi a Babban Asibitin Kula Da Masu Yoyon Fitsari, wato Abubakar Imam Urology Hospital, da ke Birnin Kano.
[…] KU KUMA KARANTA: Tarihin marubuci Abubakar Imam (2) […]