Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 49 a dajin Sambisa

1
509

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe mayaƙan Boko Haram 49 a wasu hare-hare ta sama da jiragen yaƙi na Super Tukano suka yi kan ‘yan ta’addar a jihar Borno.

An ruwaito cewa rundunar Operation Haɗin Kai ne suka kai hare-haren ta sama a ranakun 30 da kuma 31 ga watan Agusta a sansanoninsu a Gargash da Minna da Gazuwa da ke cikin ƙaramar hukumar Bama na jihar ta Borno.

A cewar wani masani kan tsaro da daƙile hare-haren ta’addanci, Zagazola Makama, a tafkin Chadi, ya ce hare-haren ta sama na ranar 30 ga watan Agusta, sun kuma faɗa kan wata babbar motar ‘yan tada ƙayar bayan da ke tafiya tare da kashe ɗaukacin waɗanda ke cikin motar.

A ranar 31 ga watan Agusta, an samu bayanan sirri da suka nuna mayaƙan na hada-hadar aikin kudi, inda nan take aka kai musu hari da kashe wasu daga ciki.

Shaidu sun ce an akshe aƙalla ‘yan ta’adda 29 a Gazuwa da kashe wasu da ke tafiya cikin mota guda hudu a Gargash, yayin da mayaka 16 kuma suka gamu da ajalinsu a garin Minna.

1 COMMENT

Leave a Reply