Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kama wani Kwale-kwale ɗauke da wasu ƙulli da ake zargin muggan ƙwayoyi ne a Ibeshe, Iworo da Badagry a jihar Legas.
Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Sub Lieutenant Happiness Collins ya fitar, ya ce, a ƙiyastacce, ƙwayoyin sun kai Naira miliyan 200, nauyinsu ya kai kilo 2,640.
Duk da cewa, waɗanda suka yi ƙoƙarin shigowa da kayan, sun tsere bayan hango jami’an sojin, amma an ƙwace kayayyakin tare da miƙa su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) domin ɗaukar matakin da ya dace.” inji sanarwar.
KU KUMA KARANTA: Kotun sojin Najeriya ta gurfanar da jami’ai 12 kan laifuka daban-daban
Collins ya kuma bayyana cewa, Kwamandan rundunar sojin ruwan da ke sintiri a yankin (NNS BEECROFT), Commodore Kolawole Oguntuga, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton sirri ga jami’an tsaron domin daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.