Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ya Sha Alwashin Ci Gaba Da Aiyukan Alheri A Fadin Yankin

0
361

Daga; Jabiru Hassan, Kano.

SHUGABAN majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa yace karamar hukumar zata ci gaba da gudanar da aiyukan alheri a fadin yankin ta yadda al’umar karamar hukumar zasu amfana da ribar dimokuradiyya bisa jagorancin sa.

Yayi wannan tsokacin ne a wata gaanawa da yayi da wakilin mu, dangane da cikar sa shekara guda kuma a karo na biyu bisa shugabancin Karamar hukumar ta Dawakin Tofa, tareda jaddada cewa da yardar Allah, kowace mazaba zata rabauta da muhimmin aiki domin kyautata zamantakewar al’uma.

Alhaji Ado Tambai Kwa ya kara da cewa sanin kowa ne cewa majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa tana kokari sosai wajen samar da romon dimokuradiyya a kowane sako da lungu na yankin, sannan ana taba kowane fanni a aikace, don haka zasu kara himma wajen ganin ana ci gaba da amfana da shugabancin su.

Dangane da irin nasarorin da suka samu kuwa, Ado Tambai Kwa ya sanar da cewa suna kokari kan harkar ilimi wanda shine ginshikin rayuwar al’uma sannan suna baiwa mata da matasa kulawa wajen samar masu da hanyoyin dogaro dakai da bada horo kan sana’oi da kuma kyautata harkokin kula da lafiya batare da nuna gajiyawa ba.

Haka kuma Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa yanzu haka suna kara yin Kokari wajen kara bullo da sahihan hanyoyi na inganta zamantakewar al’uma ta fuskar tsaro da kuma tabbatar da cewa ana bin doka da oda a fadin yankin.

Yayi amfani da wannan dama inda ya jinjinawa gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen kawo managarcin ci gaba a jihar kano, tareda kyautata tsarin tafiyar da siyasa a jihar da kuma inganta dangantaka tsakanin gwamnatin sa da majalisun kananan hukumomi wanda hakan ya taimaka wajen tafiyar da jagorancin al’uma cikin nasara.

A karshe, Alhaji Ado Tambai Kwa ya godewa daukacin al’umar karamar hukumar Dawakin Tofa saboda kaunar da suke nuna masa batare da nuna gajiyawa ba, sannan ya yabawa Yan majalisar dokoki da na zartaswa na karamar hukumar bisa yadda ake tafiya tare Kuma ake aikin al’uma batare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here