Gwamnatin tarayya ta ce ta daƙile yunƙurin wasu masu kutse daga Turai har sau 66 da suka yi yunkurin yin kitsen a tarukan majalisar zartaswa ta tarayya ke yi duk mako wato FEC.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki Farfesa Isa Pantami, ne ya bayyana haka a Abuja, a taro karo na 19 na jerin makon Gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (2015-2023) ranar Alhamis.
KU KUMA KARANTA:Daraktan Galaxy, Farfesa Muhammad Bello ya taya Ministan Sadarwa Pantami murnar samun lambar Yabo ta CIISec
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito Pantami yana cewa tun bayan bayyanar da manufar ƙasa kan harkokin kasuwanci na gwamnati a watan Oktoba na shekarar 2020, bai kai ƙasa ba, an gudanar da tarurrukan FEC guda 108.
Ya ce daga tarurrukan FEC guda 108 da aka gudanar, an yi yunƙurin kutse a tarurrukan 66 ne daga ƙasashen Turai amma an daƙile yunƙurin.
Ministan ya ce an kai rahoton dukkan shari’o’in ga hukumomin da suka dace domin yin aiki da su.