Sakkwato ba garin yin ɓatanci ga Manzon Allah (SAW) ba ne – Gwamna Aliyu

0
309

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya yi gargaɗi kan duk wani abu da zai iya ɓata darajar Annabi Muhammad (SAW), musamman a jihar, wadda galibi al’ummar Musulmi ne.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake mayar da martani game da kashe wani mahauci, Usman Buda, a kan zarginsa na yin kalaman ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran sa, Abubakar Bawa, gwamnan ya sha alwashin magance duk wanda ya yi ɓatanci ga manzon Allah.

KU KUMA KARANTA: An kashe mahauci har lahira a Sakkwato saboda zargin ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

Gwamnan, ya gargaɗi mazauna yankin da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

“Gwamnan jihar Sakkwato, Dakta Ahmed Aliyu, ya yi ƙira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda a kowane lokaci.

“Gwamnan ya ja kunnen jama’a kan duk wani abu da zai iya ɓata darajar Annabi Muhammad (SAW), musamman a jiha kamar Sakkwato, al’ummar Musulmi ne mafi rinjaye.

“Dakta Aliyu ya ce mutanen Sakkwato suna mutunta Annabi Muhammad (SAW) sosai, don haka akwai buƙatar dukkan mazauna garin su mutunta shi, su kare martabarsa da mutuntakarsa.

“Ina so in yi ƙira ga al’ummar Jihar Sakkwato da su guji ɗaukar doka a hannunsu, maimakon haka su kai rahoton duk wani laifi ko cin zarafi ga waɗanda suka dace domin ɗaukar matakin da ya dace.

“Addininmu ba ya ƙarfafa ɗaukar doka a hannun mutum, don haka mu yi ƙoƙari mu zama masu bin addininmu nagari,” in ji shi.

Bawa ya ci gaba da cewa gwamnan ya gargaɗi masu son tayar da hankali da su canza tunani, inda ya ce Sakkwato ba daidai ba ne a aikata irin wannan laifin.

Ya ce: “Gwamnatin da ke yanzu ba za ta ɗauki lamarin ɓatanci ga Annabi da wasa ba, kuma za ta hukunta duk wanda aka samu da aikata duk wani aiki da aka yi da nufin wulaƙanta darajar Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wasallama, daidai da tanadin dokokin Musulunci.

“Gwamnan ya baiwa al’ummar jihar tabbacin ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin duk ‘yan ƙasa masu bin doka da oda.

“Gwamnan ya kuma gargaɗi masu son tayar da hankali da su canza tunani, ya ƙara da cewa Sakkwato ba gurin zaman su bane.”

Leave a Reply