Sabo GRA Ta Samu Sabon Shugaba, Ya Sha alwashin Ƙarfafa Nasarar Marigayi Kwamared Silas Adamu

0
429

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAKTA Danjuma Sale ya zama sabon shugaban kungiyar al’ummar Tsaunin Kura dake Sabo GRA a cikin garin Kaduna.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar (EPRO), Okpani Jacob Onjewu Dickson, mai kwanan wata Litinin, 30 ga watan Mayu, ta ce ya fito takara ne a wani taron, wanda aka gudanar da zaben Kungiyar al’ummar a karamar hukumar Chikun a ranar Asabar 28 ga watan Mayu.

An kuma zabi Mista Patrick Fumen a matsayin Sakatare Janar, da Dattijo Zachariah A. Gyas a matsayin Babban Ma’aji da Joseph Markus Bobai (Esq) a matsayin Mataimakin Sakatare Janar.

Sauran shugabannin da zasu ci gaba da rike mukamansu na wa’adi na biyu.

Su ne; Dattijo Onojah J. Attah (Mataimakin Shugaban), Mista Apollos Shinkut (Sakataren Kudi) da Mista Cletus A. Ogbonna (Central Welfare).

Sauran su ne; Mista Emmanuel Zuahu (Mai Bincike), Okpani Jacob Onjewu Dickson (Jami’in Hulda da Jama’a “EPRO”), Misis Cecilia Dzingina (Shugaban Mata), Mista Jonah Adua Kure (Shugaban Matasa) da Sir Ben Churchill ( Esq) (Mai Bayar da Shawara Kan Shari’a).

A jawabinsa na karbar rantsuwa jim kadan bayan rantsar da sabon shugaban kasa, Dakta Sale ya sha alwashin ciyar da al’umma gaba tare da samar da goyon bayan daukacin al’umma.

Bayan bayyana irin kyawawan halaye na Marigayi Shugaban Kungiyar, Kwamared (Dr.) Silas Adamu, ya sha alwashin karfafa nasarorin da aka samu.

Leave a Reply