Connect with us

Iftila'i

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Published

on

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Aƙalla mutum uku sun rasu, yayin da wasu bakwai suka jikkata, bayan da wani gini ya rufta sakamakon mamakon ruwan sama a ƙaramar hukumar Nangere da ke Jihar Yobe.

Iftila’in ya faru ne a Tsohon Gari da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Nangere a ƙarshen wannan makon.

Majiya daga yankin ta ce sama da gidaje 50 ne suka lalace, lamarin da ya sanya mutane da dama rasa matsugunansu.

Wani mazaunin yankin, Shuwa Adamu, ya shaida wa Aminiya cewar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da iska ne ya yi sanadin rushe gidajen.

“Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe lokacin da yawancin mazauna yankin ke shirin fita kasuwa kamar kullum.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama ya lalata gidaje da gonaki a jihar Kogi

“Akalla shaguna da gidaje 50 ne suka lalace, sai kuma wani yaro ɗan shekara bakwai da ya rasu.
“Jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe sun tantance adadin asarar da aka yi a yankin,” in ji shi.

Wata mazauniyar yankin, mai suna Halima ta ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi ajalin mutum uku tare da lalata kadarori da dama.

“Sama da gidaje 50 ne suka lalace yayin da mutum uku ciki har da wani yaro ɗan shekara bakwai, suka mutu.
“Mutanen da suka rasa gidajensu a halin yanzu suna tare da danginsu,” in ji ta.

Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (Yosema) Dokta Goje Muhammad, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa.

Ya ce hukumar ta biya kuɗin kula da lafiyar waɗanda suka jikkata da ke babban asibitin Nangere.

Kazalika, ya ce an sallami waɗanda suka jikkata baki ɗaya daga asibitin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Iftila'i

Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Published

on

Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Wasu mutane da dama sun maƙale a cikin bene da ya rushe a yankin Area 11 da ke unguwar Garki.

Ranar Litinin da misalin karfe 8;30 na dare ne ginin ya rushe, jim kaɗan bayan wasu leburori da ke aiki a wajen sun tashi.

Wani mazaunin unguwar Garki, Joseph Habila, ya ce ƙarar rushewar ginin ta haifar da zullumi a tsakanin mazauna yankin.

Joseph ya ce, “Allah ne Ya kiyaye saboda Ni kaina na je na yi sayayya a kusa da ginin, ban jima sa barin wurin ba ginin ya rushe.”

Ya ce jami’an tsaron da suka kai ɗauki sun ceto mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan ginin.

KU KUMA KARANTA: Gini ya faɗo ya kashe Fasto a Benuwe

Sai dai ya ce ba zai iya tantance adadin waɗanda aka ceto ba.

Rundunar ’yan sandan Abuja ta sanar cewa an ceto mutane uku daga baraguzan.

Sanarwar da kakakin rundunar, Josephine Adeh ta fitar ta ce an garzaya da mutanen zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.

Ta ƙara da cewa an sanar da hukumomin da suka dace game da al’amarin kuma sun karbe ikon wurin da abin ya faru.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like