Labarin yana gefen ku!

Rundunar ‘yansanda ta shelanta neman Sheikh Idris Dutsen Tanshi ruwa a jallo

1

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta ayyana neman fitaccen malamin addinin musuluncin da ke jihar, Imam Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo bisa zarginsa da ƙin mutunta kotu. Kuma an sanya tukuici mai gwaɓi ga duk wanda ya tona inda malamin yake a ɓoye a halin yanzu.

‘Yansanda a wata shelar musamman da ta fitar a ranar Alhamis ta ce, umarnin ya fito ne daga ofishin sufeto-janar na hukumar, inda suka roƙi dukkanin wani ko wasu da ke da bayanin yadda za a kama Idris da ya gaggauta sanar da jami’in ‘yansanda mafi kusa da shi.

Sanarwar ta ce Idris da ake nema ruwa a jallo sama ko ƙasa ya yi ba a sani ba, Malamin yana da shekaru 62 a duniya, kuma an masa gani na ƙarshe ne a unguwar Dutsen Tanshi da ke Bauchi amma yanzu ba a san inda yake ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

“Da zarar ka ganshi, kama shi ka miƙa shi ga caji ofis ɗin ‘yansanda mafi kusa da kai ko kai tsaye zuwa ofishin mataimakin kwamishinan ‘yansanda, shafin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ko a ƙira lambobin waya; 08151849417, 09048226246.”

Rundunar ta ce akwai tukuici ga duk wanda ya taimaka musu suka cafke malamin.

Idan za a tuna dai babban kotun shari’a mai lamba 1 da ke Bauchi ta bai wa ‘yansanda umarnin cafko malamin gami da gurfanar da shi a gabanta bisa zargin da ƙin mutunta gayyatar da kotun ta masa domin ci gaba da sauraron ƙarar da ake masa kan tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiya a jihar Bauchi.

Malamin dai ya yi abun da ya ƙira ‘Hijira’ ne bayan da haɗakar jami’an tsaro suka yi wa gidansa ƙawanya da nufin kama shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.