Connect with us

Abincinka Maganinka

Ranar zuma ta duniya: Amfani da sirrikan dake tattare da zuma

Published

on

Yau ranar zuma ta duniya. Neptune Hausa ta binciko muku amfanin zuma ga ɗan adam. Ku biyo mu don sanin sirrikan dake tattare da wannan halitta ta Ubangiji.

Zuma dai kamar yadda muka sani wata halitta ce mai matuƙar tasiri a rayuwar ɗan adam. Kasantuwar ƙudan zumar yana cin furanni da kuma wasu lokutan itatuwa daban daban, hakan ne ma kashin sa da yake fitar wa ake da yakinin yana magunguna da dama a cikin jikin ɗan adam.

Mutane dai suna amfani da ruwan zumar a matsayin abinci ko magani ga cututtuka da dama. Haka ma dai an ambaci zuma a wurare da dama a cikin alkur’ani mai girma saboda muhimmancin ta.

  1. Tana taimaka ma mai-mura, tari, atishawa da sauran matsalolin sanyi.
  2. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
  3. Tana rage nauyin ƙiba. Shan ruwa mai`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage ƙiba.
  4. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
  5. Tana sauƙaƙa narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
  6. Maganin gudawa ce.
  7. Tana karfafawa garkuwar jiki.
  8. Tana gyara fata da rage ƙurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
  9. Maganin gyambon ciki – Ulcer.
  10. Tana kara kuzari.
  11. Zuma na kare mutane daga kamuwa da cutar siga wato Diabetes da turanci sannan kuma yana hana tashin cutar wa mutanen da ke fama da shi.
  12. Zuma na maganin matsalolin da ke kama ido kamar jan ido, kaikayin ido, kumburin ido da sauransu.
  13. Zuma na rage yawan mantuwa musamman matan da suka daina haihuwa.
  14. Zuma na ƙara kaifin basira da riƙe karatu musamman a yara.
  15. Yana kuma maganin cutar Ulcer.
  16. Zuma na taimaka wa mutanen(maza ko mata) dake fama da matsalar rashin haihuwa.
  17. Zuma na kuma maganin ciwon ciki.
  18. Ana amfani da zuma wajen gyaran gashi.
  19. Zuma na da amfani wajen ibadar aure da lafiyar ma’aurata.
  20. Ana amfani da zuma a maimakon sukari wajen sawa abin sha ɗanɗano.
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Da wane dalili ‘yan sanda suka lakaɗa wa ɗan Okada duka a Legas? | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Abincinka Maganinka

Amfanin abarba a jikin ɗan Adam

Published

on

Abarba na ɗaya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin ɗan Adam.

Abarba na da matukar amfani a jikin ɗan adam saboda tana ɗauke da muhimman abubuwa; fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.

Waɗannan sinadarai dai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar ɗan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.

 Kaɗan daga amfanin abarba:

KU KUMA KARANTA: Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai

  1. Tana ɗauke da sinadarin magnees da calcium wanda ke ƙara ƙarfin ƙashi
  2. Tana ɗauke da anti oxidant wanda ke ƙara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.
  3. Tana maganin mura da sanyin ƙirji.
  4. Tana ƙara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka.
  5. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.
  6. Tana ƙara lafiyar dasashi da kare haƙora.
  7. Tana sauƙaƙa yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.
  8. Tana maganin tsutsar ciki.
  9. Tana ƙara ma idanu lafiya
  10. Tana ƙara lafiyar ciki da sauƙaƙa bahaya
  11. Tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.
Continue Reading

Abincinka Maganinka

‘Ya’yan itatuwa bakwai masu kyau ga idanu

Published

on

Kula da lafiyar ido yana da mahimmanci ga lafiyar gaba ɗaya.

Duk da yake babu ‘ya’yan itace ɗaya  da zai iya tabbatar da cikakkiyar gani, haɗa nau’ikan ‘ya’yan itace masu wadatar wasu sinadarai na iya ba da gudummawa ga lafiyar ido.

Ga wasu ‘ya’yan itatuwa na yau da kullum masu amfani ga idanunku:

  1. Lemo: Lemo suna da kyakkyawan tushen bitamin C, maganin antioxidant wanda ke taimakawa kare idanu daga damuwa na iskar oxygen da macular degeneration (AMD).

KU KUMA KARANTA: Abinci guda 5 da suke gyara jikin mutum

  1. Gwanda: Gwanda na da wadataccen sinadarin bitamin C, E, da beta-carotene, waɗanda ke taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da cutar ido.
  2. Strawberries: Strawberries wani ‘ya’yan itace ne mai yawan bitamin C, wanda zai iya taimakawa wajen kiyaye lafiyar jijiyoyin jini a idanu.
  3. Mangwaro: Mangwaro tushen bitamin A da beta-carotene ne mai kyau, yana da mahimmanci don aikin ido da kyau kuma yana iya kariya daga bushewar idanu.
  4. Avocado: Avocado yana ɗauke da lutein, zeaxanthin, da kuma bitamin E, wanda zai iya taimakawa wajen kare idanu daga lalacewar shekaru.
  5. Inabi: Inabi, musamman masu launin duhu kamar ja da inabi masu ruwan hoda, suna ɗauke da resveratrol, wanda zai iya taimakawa wajen kare tasoshin jini na idanu.
  6. Kankana: Kankana shi ne kyakkyawan tushen lycopene, wanda ke da alaƙa da raguwar haɗarin haɓaka AMD. Ka tuna cewa daidaitaccen abinci yana da mahimmanci ga lafiyar gaba ɗaya, gami da lafiyar ido.

Tare da cinye waɗannan ‘ya’yan itatuwa, ku ci kayan lambu masu launi daban-daban, hatsi gabaɗaya, da sinadarai masu ƙoshin lafiya.

Continue Reading

Abincinka Maganinka

Abincin da ake nomawa a arewacin Najeriya, ya isa a ciyar da mutanen ƙasar nan – Farfesa Abdulkarim

Published

on

Daga Abubakar M Taheer

Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad ya bayyana irin damarmakin da Arewacin ƙasar ke da shi wajen noma dama ciyar da al’umma ƙasar gaba.

Haka kuma ƙasar tana da hanyoyin kasuwancin kayan abincin tsakanin ƙasashen duniya.

Farfesa Abdulkarim ya bayyana haka ne a karon farko da Masana kimiyyar Abinci suka gabatar a Jami’ar Bayero dake Kano.

Taken taron na bana dai shi ne “Samarwa Abincin da ake nomawa a Arewacin Ƙasar nan wurin zama a Kasuwannin Duniya”.

Farfesa Abdulkarim Ya bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake alfahari da ita a Afirka dama duniya baki ɗaya da Allah ya horewa ƙasar noma.

Farfesa ya bayyana irin yadda masana daga ko’ina a faɗin duniya suke gabatar da ƙasidun albarka noma da ƙasar take da shi kama daga noma Masara, Dawa, Gero, Maiwa da sauransu.

“Wanda da a ce shugabannin ƙasar nan za su haɗa hannu da masana, cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar za ta zama abun kwatance a duniya dama samun hanyoyin shigowar kuɗi ga ƙasar.

Ana ta jawabin shugaban ƙungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Arewa Maso Yamma, Dakta Zahra’u N Bamalli, ta bayyana cewa manufar wannan taron shi ne shigo da masana kimiyyar abinci daga ko’ina a faɗin Arewacin ƙasar nan domin haɓaka yankin gaba ɗaya.

KU KUMA KARANTA: WHO ta ce mutane miliyan 60 za su fuskanci matsalar abinci a Afirka

Dakta Zahra’u ta ƙara da cewa, tun asalin Arewacin Nijeriya na da tarin abinci wanda ake yin su tun iyaye da kakanni, wanda ya zama dole ga masana su rinƙa yin nazari dama fito da amfanin su domin ingantawa gami da gogayya da sauran taƙwarorinsu na duniya.

“Ya zame mana dole mu rinƙa inganta abinci gargajiya tare da shigo da dabarun alkinta yadda ake yinsu, domin kula da lafiya al’ummar dama kare su daga barazanar kamuwa da cututtuka wanda aka iya kamuwa ta hanyar rashin inganci abinci.

Idan ya zama an inganta abincin mu, aka shigo da dabaru zamani wajen yinsu, nan gaba kaɗan Arewacin ƙasar zai zama abin kwatance.

Dakta Zahra’u ta ƙara da cewa, “muna so irin wannan taron ya zama wata inuwa da za ta rinƙa haɗa, masu bincike, masana, shugabanni dama masu kamfanonin sarrafa abinci dake arewacin ƙasar nan.

Tunda farko ƙwararrun masana, daga sassa daban-daban sun gabatar da ƙasidu, haka kuma taron ya samu halartar ɗalibai daga cikin jami’o’in ƙasar nan.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like