Ramadan: El-Zakzaky Ya Tallafawa Yan Jaridu Da Kayan Abinci Da Kudi A Kaduna

0
293

Daga; USMAN NASIDI Da Mustapha Imrana, Kaduna.

A KOKARIN da yake na ganin ya tallafawa al’umma musamman Mabukata daga halin kangin kuncin rayuwa da al’umma ke fuskanta, Fitatcen Malamin addinin musulunci da ke tarayyar Najeriya Sheikh Ibrahim Yakub El-zakzaky kuma Shugaban Kungiyar (IMN), ya tallafawa wasu yan Jaridu dake Jihar Kaduna da Kayan Abinci da Kudin cefane don rage radadin kuncin rayuwa da ake fama dashi.

Da yake mikawa manema labaran a Jihar Kaduna kayan abincin, Malamin addinin Kirista Fasto Yohanna Y. D Buru, ya shaidawa yan Jaridar cewa Malam Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ne ya bashi wannan kayan abincin domin ya rabawa yan Jaridun ta yadda za su samu damar yin walwala tare da farin ciki da iyalansu a wannan watan mai albarka na Azumin Ramadana da ake ciki.

Ya kara da cewa wannan aikin rabon Kayan Abincin na daya daga cikin irin karamcin da babban malamin ke yi wajen inganta rayuwar al’umma tare da nuna kauna a duk shekara, musamman a cikin irin wadannan lokutan.

Ya ce “Kuma hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya da walwalar rayuwar Jama’a don haka Malam Zazzaky ya aiko da wannan kayan abincin a ba yan Jaridu”.

“Ko a jiya da Sheikh Ibrahim Yakubu El- Zazzaky ya bayar da kayan abinci aba matan da mazajensu suka rasu ga marayu su na tare da su a yankin Kudancin Kaduna, hakazalika a bisa ga irin yadda labaran da yan jarida suka bayar hakika jama’a da dama duk sun yi murna da farin ciki da samun labarin taimakon da aka ba dimbin jama’a.

Acewarsa, a bisa irin kokarin da yan jarida ke yi ne ya sa a halin yanzu Malam Zazzaky da kansa ya ce a kawo musu wannan kayan abincin da suka hada da Shinkafa, Masara, Dawa da Gero domin kowa ya samu sukunin yin walwala tare da iyalansa”. Inji Fasto Buru.

Ya ci gaba da cewa hakika Malam Sheikh Ibrahim Yakubu El- Zazzaky ya na godiya da irin kokarin da yan Jaridu suke yi, juma kamar yadda aka ga wannan kayan abincin nasu haka aka aika da shi zuwa wadansu Jihohin a cikin kasar nan da nufin sama wa jama’a saukin rayuwa.

A karshe, Sheikh El-Zakzaky ya roki al’umma da yin amfani da damar lokacin da ake ciki wajen Addu’o’in samun karin zaman lafiya a kasar domin hakan zai taimaka wajen tabbatar da samun zaman lafiya da ciyar da al’umma gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here