PDP Ta Tsayar Da Lawal Rabi’u A Zaben Kujerar Majalisar Wakilai Ta Mazabar Lere

0
443

Daga; Isah Ahmed, Jos.

JAM’IYYAR PDP ta sake tsayar da Tsohon Dan majalisar wakilai ta tarayya, ta Mazabar Lere da ke Jihar Kaduna, Honarabul Muhammed Lawal Rabi’u, a matsayim wanda zai tsaya mata takara a wannan mazaba, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023. Wakilan Jam’iyyar ta PDP, sun zabi Honarabul Muhammed Lawal Rabi’u ne, a wajen zaben ‘yan takarar Jam’iyyar, da aka gudanar a garin Saminaka.

Da yake bayyana sakamakon zaben a safiyar yau Litiniñ. Babban jami’in zaben Danwata, ya bayyana cewa Honarabul Lawal Muhammed Rabi’u ya sami kuru’u 16, Honarabul Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya sami kuru’u 5, a yayin da Barista Ibrahim Usman Mairiga ya sami kuru’u 12. Don haka ya ce Honarabul Muhammed Lawal Rabi’u ne ya lashe wannan zabe.

Da yake jawabi bayan kammala zaben Honarabul Muhammed Lawal Rabi’u, ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan nasara da ya samu.

Ya ce wannan nasarar da ya samu nasara ce ga dukkan magoya bayan Jam’iyyar PDP.

Ya roki wadanda suka yi takara da su zo su yi hakuri su hada kai domin jam’iyyar ta PDP ta kai ga nasara a zabe mai zuwa.

Shima a nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Lere, Muhammed Lawal Aliyu, ya yi godiya ga Allah kan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya.

Ya yi fatar sauran yan takarar, zasu rungumi junansu domin a kai ga nasara a zabe mai zuwa.

Leave a Reply