Nayi safarar miyagun ƙwayoyi ne don samun kuɗin fansar mahaifiyata — Lami Jatau

0
596

Hukumar yaƙin sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta tsare wata matafiya mai suna Jatau Lami a filin jirgin sama na Legas, bisa ƙokarinta na fitar da ƙwayoyin Tramadol 1,700 MG 225 MG.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NDLEA, Mista Femi Babafemi ne ya tabbatar da kama ta, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Babafemi ya bayyana cewa an ɗauke ƙunshin ne a asirce a cikin kayanta a tafiyar da kamfanin jirgin saman Turkiyya ya yi zuwa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.

Wadda ake zargin, mai ‘ya’ya uku, ‘yar asalin ƙaramar hukumar Zangon Kataf ce ta jihar Kaduna, amma a halin yanzu tana zaune a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, tare da iyalanta, kamar yadda wani bincike na farko ya nuna.

Ta kuma danganta matakin da ta ɗauka na safarar ƙwayar a dalilin matsin lamba na neman kudin fansa Naira miliyan 5, domin a sako mahaifiyarta daga hannun ‘yan fashin.

Leave a Reply