Hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2022

1
275

Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta Yamma, (WAEC), ta fitar da sakamakon jarrabawarta ta kammala sakandare (WASSCE) ta watan Mayu da Yuni na wannan shekara 2022.

Da yake sanar da sakamakon a hedikwatar hukumar da ke Lagos, shugabanta a Najeriya Patrick Areghan, ya ce jumullar ɗalibai 1,222,505 wato kashi 76.36 cikin dari na ɗalibai 1,601,047 da suka rubuta jarrabawar sun ci kiredit zuwa sama a akalla darussa biyar, wadanda suka hada da Ingilishi da Lissafi.

Sai dai sakamakon ya nuna cewa an samu koma-baya na sama da kashi biyar cikin ɗari na cin jarrabawar idan aka kwatanta da sakamakon bara, 2021.

Mista Areghan ya ƙara da cewa ɗalibai 1,437,629 wato kashi 89.79 cikin ɗari an kammala fitar da sakamakonsu gaba daya.

Yayin da dalibai 163,418 wato kashi 10.21 cikin ɗari suke da wasu daga cikin sakamakon nasu a hannun hukumar ba a kammala fitar da su ba, in ji shugaban.

Sai dai ya ce ana yin duk abin da za a iya domin ganin an fitar da sakamakon nasu gaba ɗaya nan da mako daya.

1 COMMENT

Leave a Reply