NAPTIP ta kuɓutar da mata 11 da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya

0
514

Hukumar yaƙi da fataucin bil-Adama ta Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin da ya kai ga safarar wasu mata ‘yan Najeriya 11 daga ƙasar.

An ceto ‘yan matan ne a makwaɓciyar ƙasar Jamhuriyar Nijar lokacin da wata ƙungiyar masu safarar mutane ke niyyar jigilar su zuwa ƙasar Libya.

KU KUMA KARANTA:Yadda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da mutane 53, suka kashe mata masu juna biyu a wasu ƙauyuka huɗu a Neja

Ƴan matan da suka kasance dukkaninsu matasa, an dawo da su gida Najeriya tare da miƙa su ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa NAPTIP reshen Sokoto.

Kwamandan NAPTIP na shiyyar Sokoto, Abubakar Tabra ya shaida wa BBC cewa jami’an hukumar kula da shige da fice ta ƙasa reshen Illela ne suka karɓi ‘yan matan a karshen makon da ya gabata, inda ya ce a yanzu sun soma bincike da nufin kamo waɗanda ake zargi da safarar ƴan matan.

Ya kuma ce ana kuma kokarin bincike don gano ‘yan uwan ƴan matan don sake haɗa su da iyalansu.Bayanan da aka tattara sun nuna cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce an sace musu wayoyinsu da kayayyakinsu a cikin dazukan Jamhuriyar Nijar, inda waɗanda suka yi safararsu suka yi watsi da su, kafin jami’an ‘yan sandan Nijar ɗin su kuɓutar da su tare da miƙa su ga jami’an shige da fice na Najeriya da ke kan iyaka.

Leave a Reply