Na Samu Amincewar Kansiloli Bisa Kudirin Tsayawa Takarar Sanata A Kaduna – Hajiya Rabi Salisu

0
321

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

YAR takarar Kujerar Sanatan Shiyyar Kaduna ta tsakiya, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim, Garkuwan Marayun Zazzau, ta bayyana cewa ta samu nasarar samun amincewar Kungiyar Kansilolin Jam’iyyar APC mai mulki a bisa kudirinta na tsayawa takarar Sanata a zaben fidda gwani da na kasa baki daya.

A zantawarta da manema labarai a garin Kaduna, Hajiya Rabi Salisu, ta kara da cewa babu gudu babu ja da baya a bisa wannan kudirin nata wanda ganin irin nasarar da ta ke samu tun a yanzu tare da samun goyon bayan wasu daga cikin iyayen Jam’iyyar musamman Kansiloli wanda su ne jagorori mafi kusa da al’umma, hakan ya kara mata kwarin gwiwa.

Acewarta, wannan shi ne karo na biyu da ta ke tsayawa takara kuma kamar yadda ta tsaya takarar tsayin daka a wancan lokacin zaben ba tare girgiza ba, haka a yanzu ma wannan karon za ta yi iya bakin kokarinta na ganin cewa hakarta ya cimma domin har sai ta ga abin da ya turewa buzu nadi ba tare da gajiyawa ba.

Ta ce “ina matukar bayyana farin cikina bisa ganin irin yadda ‘ya’yan Jam’iyyar suka nuna mun goyon bayansu a kan kudirina na tsayawa takara, domin na lura ma wasu sun nuna bacin ransu a kan jin cewa ance na janye daga takarar wanda hakan ba gaskiya ba ne, domin ina nan a kan bakata, kuma hakan yasa na riga kowa ma sayan Fom din bayyana sha’awa da ra’ayin tsaywa takarar.”

“Jam’iyyar APC a karkashin Jagorancin Malam Nasir El-Rufa’i na matukar ba da girma da girmama mata a karkashin mulkinsu wanda hakan ya sanya aka saka mata da dama a cikin tafiyar da al’amura a Gwamnatin Jihar, kuma muna alfari da ganin irin hakan ba tare da nuna banbancin Jinsi al’umma yayin gudanar da harkokin siyasar Jihar Kaduna ba.”

“Alal-hakikanin gaskiya, bayan kammala bayyana kudirorina a taron ganawa da wakilan Jam’iyyar wanda mataimakin Shugaban Kasa, kuma dan takarar Kujerar shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi, hakan ya kara harzuka ‘ya’yan Jam’iyyar ta mu na ganin cewa sun mara mun baya saboda jin irin kwarewata da Gwagwarmayar da nayi a fagen Siyasa da kuma cikin al’umma.”

“Ni mace ce wacce nake da kwarewa a fannin sasanci rikece-rikece da samar da zaman lafiya wanda hakan zai ba ni wata damar ganin cewa na tabbatar da samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Shiyyar da nake wakilta, tare da kawar da duk wata matsala na rashin tsaro da al’ummar wannan yankin suke fuskanta, kana na tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Shiyyar.

“Kuma daga cikin kudirorina akwai batun inganta rayuwar mata da yara ta yadda zasu rika dogaro da Kansu, hakazalika da tallafawa al’umma masu fama da wata nakasa na musamman domin su ma suna da hakki da bukatar sumun Ingantacciyar rayuwa, don haka nake ganin nafi kowa cancanta.”

“Sannan game da zancen da ake na cewa ko Gwamnan Jihar ya tsayar da wani dan takara, wannan batu ne kawai domin babu wani dan takarar da Malam Nasir El-Rufa’i ya tsayar a matsayin zababbe a karkashin Jam’iyyar, illa kawai lokaci ne zai tabbatar mana da hakan, kuma ina fata da addu’ar Allah Yasa ni ce zababbiyar yar takarar da Jam’iyyar za ta tsayar. ” Inji Hajiya Rabi

A karshe, Yar takarar Sanatan ta Shiyyar Kaduna ta tsakiya, Hajiya Rabi Garkuwan Marayun Zazzau, ta roki yan Jam’iyyar ta APC da su tabbatar da sun ba mata duk wata damar da ake bukata a cikin wannan tafiyar tasu wanda hakan ne zai tabbatar da adalci a cikin al’umma da yanayin gudanar da harkokin siyasar Jihar.

Leave a Reply