Na Rubuta Wannan Littafi Nawa Ne Kan Yadda Ake kiwo Don ‘Yan Uwana Manoma Su Amfana – Babangida

0
473

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu.

A TATTAUNAWAR da wakilinmu na Jihar Yobe ya yi da Malam Babangida Ahmed Potiskum wanda masani ne a kan fannin kimiyyar dabbobi a garin Potiskum cikin Jihar Yobe, kuma marubucin littafin ‘Kiwo Da Yadda Ake Yin Sa’ za kuji yadda ya  bayyana dalilan da ya sa ya rubuta wannan littafin da harshen Hausa tare da sauran abubuwa. Asha karatu lafiya.

GTK: Akwai bukatar ka bayyana wa masu karatu takaitaccen bayani kan ka? 

Babangida:- To ni dai sunana Babangida Ahmed, kuma an haife ni a garin Potiskum da ke Jihar Yobe, kuma na fara karatuna na firamari a Jihar Filato wanda daga karshe na kammala a nan Jihar Yobe, kuma a nan na yi karatuna na sakandire, daga baya na tafi Jami’ar Maiduguri inda na yi digirina na farko a tsangayar ayyukan noma a bangaren kimiyyar dabbobi, wannan shi ne takaitacen tarihina a gurguje.

GTK- Ko me ya jawo hankalin ka har ka zabi karanta wannan fanni na kimiyyar dabbobi? 

Babangida:- “To da farko dai ban kudurci karanta fannin noma da kiyo ba, na nemi na zama Likita ne tun farko wanda a tashin farko hukumar tsara jarabawar share-fagen shiga jami’o’i  JAMB ta bani damar karanta fannin likitan, amma kuma na samu tangarda da ita Jami’ar Maiduguri, shi ne sai suka bani wannan fanni da na karanta. Sannan kuma a wancan lokacin na yi ta tunanin sake dawowa neman wancan fannin da na fi bukatar fannin karatun Likita, wanda a lokacin cike yake da kalubale, sai ya zama ban samu ba. Wanda a karshe na hakura da abin da ya samu, haka na dage har raina ya karbi zabin ala dole, tare da mayar da hankali a kai kuma sai na dauki hakan a matsayin zabin da Allah SWT ya yi mun.”

GTK:- To bayan kammala karatun digirin farko a wannan fanni, ka yi tunanin amfani da shi wajen bunkasa harkokin noma da kiwo? 

Babangida:- “Alal hakikia ba zan ce a tashin farko na yi wasu abubuwa dangane da habaka aikin noma kai tsaye ba, face a fakaice saboda kamar yadda kowa ya sani shi ne, bayan kammala bautar kasa (NYSC) sai na tsunduma a aikin jarida. Na dauki wannan fanni ne saboda yadda na kasance tun a farkon rayuwata ina sha’awar rubuce-rubuce ne matuka.”

“Kuma na fara ne da wata Jarida da na kafa mai suna ‘Jakadiya’, na fara buga shafi daya ina rabata a masallatan Juma’a da sauran ofisoshin ma’aikatan Gwamnati kyauta har na fara sayar da ita kama daga naira 5 zuwa 10 har dai ta habaka ta zama Jarida kuma daga bisani ta zama ‘Mujalla.’ Baya ga haka, da na ga tafiyar ta mike shi ne na yi tunanin samar da wata sabuwar ‘Mujalla’ (Magazine) ta Turanci mai suna ‘National Epitome’ wanda a yanzu haka ni nake tafiyar da ita (Publisher and Editor-inchief), amma duk da hakan ban jefar da wannan fage nawa na noma da kiwo ba, saboda na kan yi rubuce-rubuce a wasu Jaridu a duk fadin kasar nan, dangane da abubuwan da suka shafi noma da kiwo, musamman a Jaridun Hausa da wadanda nake yi. Baya ga wannan kuma Jama’a suna neman shawarwari daga gareni kan noma da kiwo a halin da ake ciki a yanzu.”

GTK:- Lura da cewa noma da kiwo na daga cikin manyan jigon ci gaban tattalin arziki, a matsayinka na kwararre, ya za ka danganta shi da Jihar ka ta Yobe kasancewar Jiha ce da mafi yawan al’ummar ta manoma ne kuma makiyaya?

Babangida:- “Alal hakika, noma da kiwo suna daga cikin abubuwa masu muhimmancin da ya dace Jama’a su kalle su da idon basira. Kuma kamar yadda ka bayyana cewa su ne jigon ci gaban tattalin arzikin kowace kasa, wanda bisa gaskiyar magana mu a nan Jihar Yobe, ana samun ci gaba ta wannan fanni, saboda duk mutumin da ya san yanayin rayuwar al’ummar wannan Jihar zai ga canji idan an kwatanta da shekarun baya.”

A baya kusan magabatan mu sun fi raja’a a harkokin noma, amma sakamakon ci gaba da wayewar da aka samu yanzu za ka tarar matashi ya zage dantse ga harkokin noma, kuma abin sha’awa shi ne yadda matashi kan noma amfanin da ya zarta yawan iyalin shi. Kuma sai ma ka tarar da matashi ya na noma buhuna daruruwa, abin gwanin ban sha’awa, idan mun dawo ta fannin Gwamnatin Jihar, musamman karkashin Gwamna Mai Mala Buni, za mu ga yadda ya yi shirye-shirye masu kayatarwa tare da bunkasa harkokin noma, saboda ina daya daga cikin wadanda Gwamnati ta tura nemo sahihan bayanai kan harkokin noma a karkashin Kwamishiniyar Ma’aikatar Noma, Dakta Hajiya Mairo Amshi, hakika na ga akwai ci gaba sosai idan an kwatamta da shekarun baya, wanda idan abin ya dore akwai dimbin nasarori.

To amma duk da haka akwai manyan kalubalen da manoma ke fuskanta su ne a halin da duniya ta ci gaba, harkokin noma sun wuce aikin fartanya ko hannu kamar da, akwai bukatar tafiya dai-dai da zamani, shi ne ya sanya na yi cikakken bayani a cikin littafin da na rubuta dangane da mayar da hankali wajen sauya salon yadda ake gudanar da noma daidai da zamani. Ka ga kenan akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo kayan noma na zamani tare da raba su ga manoma na gaskiya, kuma a guje aringizo a fannin, tare da tabbacin abin ya shiga hannun manoman gaskiya kamar yadda na ambata.

GTK:- Za mu so mu  ji bayanin abin da wannan littafi da ka rubuta ya kunsa ciki? 

Babangida:- A gaskiya shi wannan littafin da na rubuta wanda zancen da nake da kai yanzu ya karade lungu da sakon Najeriya tare da bayyana gamsuwa da alfanun da ya kunsa, musamman manomanmu a yankunan karkara da birane. Wannan littafi wanda na saka masa sunan: “Kiwo Da Yadda Ake Yin Sa” ya tattaro bayanan yadda ake kiwo ne a zamanance kuma a saukake, kuma ya zo ne sakamakon yadda na dauki dogon lokaci ina rubuce-rubuce a Jaridun kasar nan dangane da noma da kiwo, shi ne Jama’ar da ke bibiyar wadannan rubuce-rubuce su ka bukaci samar da littafin da zai kunshi bayanai dalla-dalla don amfanar da Jama’a tare da haskaka hanya a fannin kiwon wanda bayan nazari da na yi na amince da wannan bukata tasu kuma cikin taimakon Allah na yi nasarar wallafa shi a wannan shekara Kuma ya kunshi shafuka 168. 

GTK:- Wadanne kalubale ka fuskanta a yayin rubuta littafin da ma bayan kammala shi? 

Babangida:- To alal hakika, munsan a duk lokacin da ka kudurci aiwatar da wani abu na ci gaba dole ka hadu da kalubale, amma daga cikin kalubalen da na fuskanta akwai batun fassara kalmomin kimiyya na Turanci ko Girkanci zuwa Hausa, wannan ya bani wahala kwarai da gaske, musamman da yake ni ba Bahaushe ba ne. Kalubale na biyu shi ne batun kudin buga wannan littafi, wanda ya sanya na yi ta fadi-tashin nemo wata kungiya mai zaman kanta ko NGOs masu gudanar da harkokin noma da kiwo domin su dauki dawainiyar buga littafin su raba shi ga al’umma, amma abin ya ci tura- sannan kuma na bi duk hanyoyin da suka dace wajen neman Gwamnati don ta dauki nauyin buga littafin shi ma abin ya faskara. Dole ya jawo na shiga na fita wajen neman kudin da zan buga littafin da su kuma na sha wahala sosai kuma shi ne ya kawo tsaiko wajen fitar littafin. 

Kuma idan zan gaya maka adadin kudin da na kashe wajen buga littafin da kuma yadda ake sayar da shi a kasuwa za ka sha mamaki, saboda babu wata riba face kawai sadaukarwa ce. Kuma zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin Gwamna Mai Mala Buni ya taimaka a dauki nauyin buga littafin tare da raba shi ga al’umma.

GTK:- Me ya ja hankalinka na rubuta littafin kuma ya baka sha’awar rubuta shi da harshen Hausa?

Babangida:- Babban abin da ya ja hankalina na rubuta wannan littafi da harshen Hausa shi ne idan ka duba kaso 80 cikin dari na manoma a wannan yankin na Arewacin Najeriya sun fi amfani da harshen Hausa a kan Turanci, kuma mafi yawan rubuce-rubucen da aka wallafa a wannan fanni a baya da harshen Turanci aka yi su. 

Kuma har yanzu babu wani canjin azo a gani da aka samu dangane da yadda ake gudanar da harkokin noma da kiwo. Sai na ga cewa su din nan, ko da a kasuwar dabbobi ka je za ka tarar cewa wadannan manoman ne wadanda ba sa jin Turanci ko magana dashi face Hausa. 

Abu na biyu kuma shi ne, har yanzu dai wadannan mutanen suna iya karatun Hausa na boko kuma za su iya karanta littafan amma ko bihin na Turanci bai sani ba, saboda haka za su yi maraba da wannan littafi. Wannan ya na daga cikin abubuwan da su ka ja hankalinka wajen rubuta wannan littafi da harshen Hausa. Sannan kuma kamar yadda na fada da farko, na wallafa shi ne domin taimaka wa al’ummarmu ta ci gaba tare da bunkasa harkokin tattalin arzikin Jihar mu da kasa baki daya.

GTK:- Yanzu da a ce Gwamnatin Jihar Yobe ta bukaci ta ba ka dama wajen sake wallafa littafin me za ka ce? 

Babangida:- “To a gaskiya in da zan samu haka lalle zan bai wa Gwamnatin Jihar Yobe cikakken goyon baya idan har za ta nuna sha’awar wallafa littafin tare da raba shi ga al’umma. Saboda dama babban burina shi ne ya shiga hannun manoma kuma ya amfane su sannan a samu bunkasar tattalin arzikin Jihar Yobe. Saboda haka ina maraba da kowane lokaci idan gwamnatin Jihar Yobe za ta bukaci in bata don wallafa wa ko kuma ta bukaci na fadada shi, zan yi nan take domin a samu karin amfanuwa a shirye nake, saboda babban burinmu shi ne a ci gaba a matsayin mu na ‘ya’yan Jihar Yobe masu kishin ci gabanta matuka.”

Leave a Reply