Limamin Kafanchan Sheikh Adam Tahir, Ya Rasu Ya Na Da Shekaru 130

0
333

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

LIMAMIN babban masallacin garin Kafanchan a cikin Jihar Kaduna ya rasu ya na da shekaru 130.

Kamar yadda muka samu bayani cewa Shaikh Tahir, ya rasu ya na da shekaru 130 kuma ya bar yaya 26,Jikoki 290 da jikaro 200.

Mataimakin Limamin na Kafanchan, Alhaji Muhammad Kassim, ya tabbatar da cewa Shaikh Adam Tahir, ya yi fama da rashin lafiya na wani dan tsawon lokaci a Yammacin ranar Laraba.

Kassim ya ci gaba da cewa hakika an yi babban rashi musamman ga al’ummar musulmi kasancewarsa mutum abin koyi ga kowa.

A sakonsa na ta’aziyya, Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammadu II, ya bayyana rashin babban Limamin matsayin wani babban rashi ga masarautar da kuma mutanen Kudancin Kaduna.

Muhammad ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa babban Limamin ya azurta shi da samun Aljannah madaukakiya.

Leave a Reply